ElBaradei zai fuskanci tuhumar cin amanar kasa

Mohamed ElBaradei, tsohon mataimakin Shugaban kasar Masar, a Gwamnatin soja da ta hambarar da Muhammad Mursi, zai fuskanci tuhumar shari’a, bisa laifin cin amanar kasa. Wanda ya gabatar da kara, wani Farfesa ne masanin shari’a a Alkahira. Don haka kotu za ta saurari karar a ranar 19 ga Satumbar bana.ElBaradei, wanda tsohon Shugaban Hukumar makamashin […]

ElBaradei zai fuskanci tuhumar cin amanar kasa

Mohamed ElBaradei, tsohon mataimakin Shugaban kasar Masar, a Gwamnatin soja da ta hambarar da Muhammad Mursi, zai fuskanci tuhumar shari’a, bisa laifin cin amanar kasa. Wanda ya gabatar da kara, wani Farfesa ne masanin shari’a a Alkahira. Don haka kotu za ta saurari karar a ranar 19 ga Satumbar bana.
ElBaradei, wanda tsohon Shugaban Hukumar makamashin nukiliya na Majalisar dinkin duniya ne, kuma Shugaba ne a Jam’iyyar da ba ruwanta da addini, wato NSF. Saboda shahararsa a gungun wadanda suka yi zanga-zangar kawar da Gwamnatin Shugaba Muhammad Mursi, sai aka nada shi mataimakin shugaban kasa, a ranar 3 ga watan Agusta. Kuma a ya rubuta takardar yin murabus dag amukwaminsa bayan da sojojin kasar suka rika kashe magoya bayan Mursi, inda ya bayyana cewa ba zai iya daukar nauyin wannan mummunan aiki da aka aikata ba.
Wanda ya gabatar da karar, Sayyed Ateek, Farfesa Shari’a a Jami’ar Helwan, ya ce: “an nada shi mukamin ne a matsayinsa na wakilin jam’iyyar NSF da  kuma sauran al’umma da suka rattaba hannu kana yrjejeniyar Tamarod,” kamar yadda ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.
Dokta ElBaradei an danka masa amanma, don haka sai ya tuntubi wadanda suka ba shi aman kafin ya yi murabus,” inji shi.

…Kotu ta saki tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak

Shugaba Hosni Mubarak a cikin kejiWata kotu a kasar Masar ta bayar da umarnin a saki tsohon Shugaban kasar, Hosni Mubarak. Sai dai har yanzu ba a fayyace ba, kan ko an sake shi ke nan, ko kuma da sauran tuhuma.
A da, da an yi yunkurin sakinsa, sai masu gabatar da kara su bijiro da sababbin tuhume-tuhume, ta yadda suka sanya aka ci gaba da tsare shi.