Elon Musk ya tafka asara mafi girma a tarihi
Mista Musk a yanzu arzikinsa ya kai dala biliyan 178 a cewar Forbes.
Hamshakin attajirin nan, Elon Musk ya kafa tarihi bayan tafka asara irinta mafi girma na arzikin wani attajiri a duniya.
Daga watan Nuwamba 2021 zuwa Disamba 2022 ya tafka asarar dala biliyan 165, kamar yadda yake kunshe a bayanan kudin bajinta na Guinness World Records.
- Kotu ta tsare matashin da ya kashe kanwarsa da matar babansa
- Zan mayar da wa’adin sakamakon JAMB shekaru 4 —Kwankwaso
An samu wadannan alkaluma ne bisa bayanan da mujallar Forbes ta wallafa, sai dai Guinness ya ce akwai majiyoyin da ke ganin asarar na iya wuce yadda ake gani a yanzu.
Wannan ya biyo bayan karyewar hannayen jarin Mista Musk a kamfaninsa na kera motoci wato Tesla bayan sayen shafin Twitter a bara.
Sayen kamfanin Twitter kan dala biliyan 44 da Musk ya yi ya jawo hankula sosai, inda ake ganin Musk ya rage mayar da hankali ko bai wa kamfaninsa na Tesla lokaci.
Asarar da Musk ya tafka daga watan Nuwamba 2021 ya zarce wanda ake ganin ita ce mafi girma a tarihi, da Masayoshi Son ya yi a 2000 na dala biliyan 58.6.
Asarar da ya tafka an kiyasata ta ce bisa yawan hannun jarinsa, wanda kuma yana iya farfadowa, ma’ana arziki Mista Musk na iya dawowa.
A watan Disamba, Shugaban kamfanin Tesla ya rasa matsayinsa na wanda ya fi kowa arziki a duniya, bayan Bernard Arnault mallakin Louis Vuitton ya maye gurbinsa.
BBC ya ruwaito cewa tattalin arzikin Tesla ya sauka da kashi 65 cikin 100 a 2022, saboda rashin taka rawar gani.
Kamfanin ya kera motoci miliyan 1.3 a cikin shekara, kasa da abin da ake hasashe.
Sai dai saye Twitter da Mista Musk ya yi – wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce bayan korar akasarin ma’aikatansa da kawo sabbin sauye-sauye – na daga cikin dalilan koma bayan da ya fuskanta.
Masu hannun jari da dama a Tesla na ganin akwai bukatar ya mayar da hankali wajen sake farfado da kamfanin, yayin da bukatar motar ke karuwa ga kuma matsalolin tattalin arziki, karuwar goggayar kasuwanci da matsalolin da annobar Coronavirus ta haifar.
“Irin wannan kamfani da aka dau lokaci wajen kafa shi na da muhimmanci. Haka zalika ruɗanin kasuwanci na iya haifar da komai,” kamar yada Mista Musk ya wallafa a shafinsa bayan kawo karshen bayanan kasuwar ciniki a Disamban 2022.
Mista Musk a yanzu arzikinsa ya kai dala biliyan 178 a cewar Forbes, yayin da Bernard Arnault ke da dala biliyan 188.