Elon Musk ya yi barazanar fasa sayen Twitter

Ya ce matukar ba a daddale bayanan ba, cinkin zai iya tashi

Elon Musk ya yi barazanar fasa sayen Twitter

Elon Musk

Attajiin nan da duniya, Elon Musk, ya yi barazanar fasa cinikin shafin sada zumunta na Twitter wanda ya saya a kan Dalar Amurka biliyan 44 saboda gaza ba shi wasu muhimman bayanai.

A wata wasika da lauyoyinsa suka fitar a ranar Litinin, attajirin ya ce matukar ba a ba shi wasu cikakkun bayanai kan shafukan bogi da ke dandalin ba, akwai yiwuwar cinkin ya sami matsala.

Hakan dai a cewarsa ya saba da yarjejeniyar da suka kulla da su tun a farko.

“Wannan karara ya saba da matsayar da muka cim ma da su ta samar da bayanai ba tare da kumbiya-kumbiya ba,” inji shi.

Sai dai kamfanin na Twitter a cikin wata sanarwa ranar Litinin ya ce yana fatan ganin cinikin ya kammala a kan farashin da aka amince tun da farko.

A watan Afrilun 2022 ne Hukumar Gudanarwar Twitter ta amince da murya daya ta sayar wa Elon Musk dandalin, ko da yake yarjejeniyar ta bukaci amincewar masu hannun jari a kamfanin.

A wata sanarwa yayin sayen kamfanin dai, Elon Musk ya ce dakatar da amfani da shafukan bogi ne zai kasance cikin manyan abubuwan da zai fi mayar da hankali a kan su da zarar cinikin ya fada.

Sai dai a watan da ya gabata, attajirin ya sanar da jinkirta kammala cinikin har sai an daddale batun.