Elon Musk ya zama na farko da dukiyarsa ta haura tiriliyan
Sabon matsayinsa ya biyo bayan gagarumin sayar da hannayen jarin kamfanin SpaceX, wanda ya ƙara darajar kamfanin da kuma yawan kuɗin da Musk ke da su
(FILES) Elon Musk looks on during a news conference with US President Donald Trump in the Oval Office of the White House in Washington, DC, on May 30, 2025. Musk has urged his 227 million social media followers to cancel their Netflix subscriptions, accusing the streaming platform of promoting what he describes as transgender propaganda. In his latest culture war campaign, the Tesla tycoon joined a trend launched by conservative social media account Libs of TikTok that cited the animated series “Dead End: Paranormal Park” and Netflix’s corporate diversity efforts as a cause for dropping the streaming service. (Photo by Allison ROBBERT / AFP)
Attajirin nan kuma shugaban kamfanonin fasaha, Elon Musk ya zama mutum na farko a tarihi da dukiyarsa ta haura Dalar Amurka tiriliyan ɗaya.
Sabon matsayinsa ya biyo bayan gagarumin sayar da hannayen jarin kamfanin SpaceX, wanda ya ƙara darajar kamfanin da kuma yawan kuɗin da Musk ke da su a ciki.
- Bayan yunƙurin sasanci da ’yan bindiga sun kai hari a Katsina
- An kama jami’in tsaro kan zargin safarar zinaren ₦4.4bn a Kano
Rahotanni sun nuna cewa, darajar dukiyar Musk yanzu ta zarce dala tiriliyan 1.1, inda kaso mai tsoka daga cikinta ya fito ne daga hannayen jarinsa a SpaceX, waɗanda aka ƙiyasta darajarsu ta kai kusan Dala biliyan 866.
Wannan ci gaban ya sa Musk ya ƙara nisa da sauran attajiran duniya, inda mutumin da ke biye da shi a jerin masu kuɗi ke da dukiya kusan dala biliyan 300 kacal.
Musk ya yi fice ne ta hanyar kamfanoninsa da suka haɗa da: Tesla, SpaceX da kuma X, waɗanda suka yi tasiri a fannoni kamar motocin lantarki, zirga-zirgar sararin samaniya da sadarwar zamani.
Sai dai nasarorin nasa na ci gaba da jawo muhawara, inda wasu ke nuna damuwa kan yadda ƙarfin tattalin arziki da tasiri ke ƙara taruwa a hannun mutum guda.