Emeka Ani: Ibo Kirista hadimin Shugaban Boko Haram

‘Tare muke zuwa kwallon kafa da Muhammad Yusuf’
‘Ya yi karatun boko sosai’

Emeka Ani: Ibo Kirista hadimin Shugaban Boko Haram

Chukwuemeka Emmanuel Ani

  • ‘Tare muke zuwa kwallon kafa da Muhammad Yusuf’
  • ‘Ya yi karatun boko sosai’

Chukwuemeka Emmanuel Ani, wanda aka fi sani da Emeka, dan kabilar Ibo ne kuma Kirista da ya dade yana hidima ga jagoran Boko Haram na farko, Muhammed Yusuf. Aminiya ta zanta da shi kan alakarsa da Mohammed Yusuf da Abubakar Shekau da sauransu:

Yaya alakarka take da Muhammed Yusuf?

Yana kaunata matuka. Muhammed Yusuf mutum ne mai saukin kai. Yana yawan ba mu shawarar mu yi kokari mu zama ababen koyi. Yana da barkwanci, amma ba ya daukar raini.

Idan ya ga mace ta saka wando, yakan kira ta, ya ce mata babu kyau. Wata rana muna dawowa daga atisayen kwallon kafa, sai ya ga wasu suna fada, sai ya tsaya ya sulhunta su.

Don haka lokacin da rikicin Boko Haram ya taso, sai na shiga mamakin yadda rikicin zai faro daga mutumin da nake kallo a matsayin abin koyi, domin ina son kwallon kafa kamarsa. Ya kasance gola ne mai kyau.

Yaya Shekau fa?

Ba ni da kusanci da Shekau sosai saboda yana da zafi sosai, amma shi ma yana kaunata. Shi ba ya buga kwallo, amma yana raka Muhammed Yusuf filin kwallo. Su biyun duka suna da ilimi, amma daga baya suka canja hanya.

Yaushe ne karshe da ka ga Shekau?

Kwanaki kadan bayan an kashe Muhammad Yusuf lokacin da ake yunkurin rushe markaz dinsa. A cikin dare ne, sai ya sa aka kira ni, ya fada min cewa ba zan sake ganinsa ba. Sai ya tafi.

Sun taba cewa ka guji karatun boko?

Ba su taba ba cewa in daina karatu ko koyar da boko ba. Muhammad Yusuf yana da ilimin boko sosai. Yana da digiri na biyu, kuma yana umartar mu cewa mu yi karatu.

Amma sun taba yunkurin sauya tunaninka ka zama dan ta’adda?

Ba su taba ba, amma akwai abokai da muke tare da su da suka rika takura min in bi su daji bayan an kashe shi. Kafin a kashe shi amma ya taba fada min kada in damu, in zauna babu abin da zai same ni. A lokacin mahaifina yana da rai, sai Muhammad Yusuf ya fada wa mahaifin nawa cewa kada ya damu. Da rikicin ya yi kamari bayan kashe shi, sai takurar ta fara yawa a kan lallai dole in bar addinina in bi su daji, wanda hakan ya sa na tsere daga garin.

Kai Kirista ne, amma ka bayar da makarantarka ana karatun Musulunci, me ya sa?

Mutanen ne suka zo, suka ce suna son ginin domin karatun Islamiyya, sai na ce musu ai dukkanmu Allah muke wa bauta. Suka tambaya nawa za su rika biyan kudin haya, na ce musu kyauta na ba su.

Yanzu kusan shekara bakwai ke nan. Amma daga baya sai na fara fuskantar kalubale daga ’yan uwana Kirista wadanda suke ganin bai kamata in bayar da gidan ana karatun Islamiyya ba, wanda hakan ya sa suka fara cire yaransu daga makarantata ta boko, shi ya sa makarantar ta rage dalibai sosai.

A da muna karatun safe da yamma, amma yanzu na daina na yamma saboda a samu damar yin karatun Islamiyya.

Shekara nawa ke nan kana zaune a nan?

Na yi akalla shekara 20. Wannan ya sa na yi tunanin me zan yi in taimaki yankin, sai na ga tunda ina da ilimin boko, gara in fara koyarwa domin a karu da ni. Hakan ya sa muka hada hannu da wani Malam Bashir da sauransu domin taimakon al’umma.

An ce da makarantarka tana kusa da Markaz din Muhammad Yusuf ne, me ya sa ka canja waje?

Wancan ginin haya nake yi. A lokacin da rikicin Boko Haram ya yi zafi, sai aka bata ginin, wanda hakan ya sa na gudu daga wajen na buya.

Wadanne kalubale ka fuskanta bayan ka dawo?

Bayan na dawo, sai sojoji suka ce ba zan yi amfani da wajen domin ci gaba da makarantata ba, inda suka ce zan iya yin amfani da wajen in rika boye ’yan Boko Haram a ciki suna hada bama-bamai.

Suka ce Ibo suna da wayo da wayewa, kuma za su iya yin komai. Sai na ce musu su tambayi mutanen yankin game da ni. Amma suka ce lallai ba zan dawo wajen ba. Wata rana sai aka ce sojojin suna kirana, sai na samu mutanen yankin a wajen sojojin, inda suka bayar da shaida mai kyau game da ni.

Sai na sake bude makarantar da dalibai 8 a ranar 13 ga Oktoban 2016, sai kuma a shekarar 2017 muka bude Islamiyya.

Yanzu dalibanku nawa?

Kafin mu bude sashen Islamiyya, muna da dalibai 200 ne, amma daga baya sai wasu daga cikin Kiristoci suka cire yaransu daga makarantar, wanda hakan ya sa yanzu daliban ba su kai 100 ba.

Kuma har yanzu ba mu kara kudin makaranta ba daga Naira 3,500 da muke karba a duk zangon karatu domin nan yankin marasa karfi ne. Yawancin mutanen yankin manoma ne da kananan ’yan kasuwa. Don haka idan ka kara kudin makaranta, ba za su iya biya ba.

Hakan ya sa muke fuskantar kalubale, amma a haka muke kokartawa.

Yaya kake ganin rayuwa bayan barkewar rikicin Boko Haram?

Tun bayan rikicin, na je wurare da dama kafin in dawo Maiduguri, inda a yanzu na fi samun natsuwa domin duk a wannan yankin, tun daga Abbaganaram da State Low Cost zuwa nan, kowa ya san ni. Ina da saukin mu’amala da kowa.

Wannan ya sa nake kokarin koyarwa a matsayin wata hanyar taimakon marasa karfi tunda ba ni da dukiya.

Ina jin dadin yadda nake ganin daliban suna samun karatu a kusan kyauta. Ina son yara sosai. A gaskiya ina jin dadin aikin da nake yi.

Ka kasance tare da manyan jagororin Boko Haram, yanzu kuma kana rayuwa da wadanda Boko Haram suka illata, yaya kake ji?

Babbar hanyar da za a bi wajen magance wannan matsalar ita ce a rika sauraron malamai. Idan muka bar rikici, da tu’ammali da miyagun kwayoyi, za a samu saukin rikice-rikicen nan da ake ciki, musamman ma shan kwayoyi.

Ke nan ’yan Boko Haram suna shan kwayoyi?

Su ma mutane kamar mu, wasu daga cikinsu rashin aikin yi ya kai su shiga Boko Haram da kuma rashin ilimi. Wadannan matsaloli suna cikin dalilan da suka sa na ce akwai bukatar in yi amfani da wannan waje domin ilimantar da yaranmu.

A Maiduguri aka haife ka?

Kwarai kuwa. An haife ni ne a Arewacin Shehuri.

Iyayenka fa?

Mahaifina Pedro ya rasu, amma har yanzu ina tare da mahaifiyata da ta tsufa sosai. Ni ne babban da a gidanmu, sannan mu bakwai ne. Ina da mata da ’ya’ya biyu. Matata Margi ce ’yar Borno.

Wane tallafi kake ganin kana bukata?

Babu tallafin da nake bukata kamar na kudi. Ginin ya fara tsufa, kuma ni kadai na gina shi, amma ba zan manta da tallafin masu kula da bangaren Islamiyya ba, domin sun ba ni tallafin siminti da yashi. A bangaren malamai, muna da kwararrun malamai da za su koyar da boko da Islamiyya da kyau.