Emmanuel Adebayor ya Musulunta
A ranar Lahadin da ta wuce ne aka samu labarin Musuluntar Emmanuel Adebayor, shahararren dan kwallon Togo da yanzu haka yake buga wa kulob din Tottenham na Ingila kwallo. Rahoton da kafar sadarwar naij.com ta kalato ya nuna an ga dan kwallon yana karbar shahada don shiga addinin musulunci ne a Togo watau kasar haihuwarsa.Haka […]
A ranar Lahadin da ta wuce ne aka samu labarin Musuluntar Emmanuel Adebayor, shahararren dan kwallon Togo da yanzu haka yake buga wa kulob din Tottenham na Ingila kwallo.
Rahoton da kafar sadarwar naij.com ta kalato ya nuna an ga dan kwallon yana karbar shahada don shiga addinin musulunci ne a Togo watau kasar haihuwarsa.
Haka kuma labarin Musuluntar dan kwallon ta yadu a shafin abota na facebook da na twitter da sauransu inda jama’a suka rika baza labarin.
Kimanin watanni biyu da suka wuce ne dai dan kwallon ya rika bayyana sabanin da ke tsakaninsa da iyalansa da suka hada da mahaifiyarsa da kuma kaninsa Rotimi a shafin abota na facebook da wasu kafofin watsa labarai. dan kwallon ya bayyana takaicin yadda iyalansa suka rika yi masa bita-da-kulli duk kuwa da irin taimakon da ya yi musu. Hasalima ya bayar da misali da yadda kaninsa Rotimi ya sace wa wadansu mutane agogo da wayoyin hannu masu tsada akalla 30 a lokacin da ya gayyace shi Ingila don ya zauna da shi.
A wani labari makamancin wannan, Emmanuel Emenike dan kwallon Najeriya Super Eagles ya karyata rade-radin da ake yi na cewa ya karbi addinin Islama. dan kwallon ya ce babu kanshin gaskiya a labarin da wasu kafofin watsa labarai suka baza na cewa ya musulunta. Hasalima yana nan a addinin Kirista kuma yana bin akidar Katolika ce kamar yadda wadanda suka sanshi za su shaida.
An rika baza labarin cewa ya musulunta ne bayan an ji wata hira da ya yi da kocinsa na kulob din Fernebache da ke Turkiyya bictor Periera inda ya shaida masa cewa yana bayan kocin ya nemi ya halarci wurin da suke karya kumallo da safiyar ranar Asabar da ta wuce amma dan kwallon ya ce masa yana azumi.
Wannan kalami ne ya sa wadansu suka dauka dan kwallon ya Musulunta, amma daga baya ya karyata batun, kuma ya ce don ya nuna yana azumi hakan ba shi ke nuna cewa ya karbi addinin Musulunci ba.