#EndSARS: A gaggauta kamo Nnamdi Kanu —Shugaban Fulani

Aminiya ta tattauna da Alhaji Sale Bayari, Shugaban Kungiyar Ci Gaban al’ummar Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah, kan zanga-zangar #EndSARS inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar kamo Shugaban Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biyafra, Nnamdi Kanu, saboda miyagun kalaman da ya yi, kan zanga zangar.   Me za ka […]

#EndSARS: A gaggauta kamo Nnamdi Kanu —Shugaban Fulani

Zanga-zangar #EndSARS

Aminiya ta tattauna da Alhaji Sale Bayari, Shugaban Kungiyar Ci Gaban al’ummar Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah, kan zanga-zangar #EndSARS inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar kamo Shugaban Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biyafra, Nnamdi Kanu, saboda miyagun kalaman da ya yi, kan zanga zangar.

 

Me za ka ce game da abin da ke faruwa a kasar nan, kan zargin sashin tsaro na SARS da cin zarafin jama’a?

Kamar yadda ’yan Najeriya da dama suka sani, harkar jami’an tsaro a Najeriya, ta zama abu mai sarkakiya.

Saboda dan Najeriya ba mutum ne da ya san muhimmancin dimokuradiyya ba.

Kowa yana ganin an ba shi dama ce, irin wadda dimokuradiyya take kawowa.

Ya dauka an bude masa hanya ce, da zai yi amfani da ita, ya musguna wa abokin gabarsa da duk wanda ba ya so.

Shi ya sa da muka samu kanmu cikin dimokuradiyya kusan shekara 20 da suka gabata, ya zamo jami’an tsaro idan abubuwa suka taso, aikin yakan zamo musu da wahala.

Dole suke barin ka’ida su yi amfani da karfi, wajen musguna wa mutane.

Don haka ya zamo ’yan SARS din nan, saboda faduwar doka a kasar nan, maganar tsaro ta zamo da wahala.

Ya zamo su kansu, suna son su rike ayyukansu kada a ce, sun gaza.

Wani lokaci wasu abubuwan da suke yi ba laifinsu ba ne, domin Najeriya kasa ce da duk wani mai bin ka’ida, sai an ga bayansa.

Saboda haka suka rika musguna wa mutane, musamman al’ummar Fulani.

Babu shakka wadansu a cikinsu, mutanen kirki ne, wadansu kuma ba mutanen kirki, ba ne.

Dama mun san cewa wannan abu da ya samu sashin tsaro na SARS, ko ba dade ko bajima tura za ta kai bango.

 

Me za ka ce kan zanga-zangar da ake yi kansu da abubuwan da suka biyo baya?

To, abin yana da kyau, kuma ba ya da kyau.

Abin da ya sa na ce haka shi ne, wani lokaci idan abubuwa suka baci, mutanen kirki suna gaya wa gwamnati cewa abubuwa sun baci.

Amma miyagun fadawa da suke jikin gwamnati, ba za su bari gwamnati ta san gaskiya ba.

Duk abin da wani mutum zai fito ya fada musu, ba za su a saurare shi ba.

Wadannan abubuwa da suke faruwa, sun nuna wa gwamnati cewa abubuwa ba sa tafiya kamar yadda suka kamata.

Domin a da ba su yarda abubuwa sun lalace ba, sai yanzu da wannan abu ya faru.

Don haka wannan zanga-zanga da ake yi, ta nuna wa wannan gwamnati cewa akwai abubuwa da yawa da ba sa tafiya daidai.

Yanzu ya rage ga gwamnatin ta san abin da za ta yi.

 

Wadansu na zargin zanga-zangar ta tashi daga manufar da ake yin ta, ta koma kamar adawa da gwamnatin, me za ka ce?

Ai duk mai hankali ya san akwai wani abu daban, kan wannan zanga-zanga.

An fara zanga-zangar ce tsakani da Allah saboda cin mutuncin da ’yan SARS suke yi ga mutane.

To amma duk wanda ke kasar nan a shekara biyar da suka gabata, ya san akwai kiyayya da bangaranci da kabilanci da adawa, kan wannan gwamnati.

Idan wadansu ba su sani ba, mu al’ummar Fulani makiyaya a Najeriya mun sani.

Saboda Fulaninmu da suke yankin Neja Delta da yankin Yarabawa da yankin Igbo, ana cin mutumcinsu ana korarsu, saboda suna Fulani.

Hukumomi ba su sani ba, idan sun sani ma, masu yin wannan abubuwa sun fi karfinsu, saboda gungun ’yan iska ne kuma ’yan ta’adda.

Mu mun san cewa akwai manufofi da dama da ake ganin cewa wannan gwamnati kamar ta Fulani ce.

Saboda shugaban gwamnatin Bafulatani ne, kuma ba za a iya zuwa a same shi a fadarsa ba, don haka idan aka samu Bafulatani a daji, sai a ce wannan Bafulatani ne sai a yi masa komai.

Don haka Fulani suka shiga cikin bala’i a kasar nan.

Shi kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tunda ya hau kan mulkin kasar nan, shekara biyar da suka gabata bai yi wa Fulani komai ba.

Amma a wannan zanga-zanga da ake yi ba mu shiga ba, domin ba za mu yi wa namu zanga-zanga ba, haka muka tsaya muna kallo.

Shugaban Kasa ya yi abubuwa da dama na tallafa wa ’yan kasuwa da manoma, amma babu abin da aka yi wa Fulani makiyaya.

Idan ana maganar noma a kasar nan, ba a maganar Fulani makiyaya, masu kiwon dabbobi.

 

Me za ka ce kan kudirin da gwamnati ta yi na biyan diyya ga wadanda jami’an SARS suka zalunta?

Biyan diyya na da kyau, amma na tabbata da za a yi lissafi a Najeriya, wadanda suka jawo wannan bala’i da muka shiga akalla za a iya ba su kashi 75.

Mu kuma idan za mu samu, watakila mu samu kashi 25, idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya tashi haka ba a ba mu komai ba, saboda mu komai muna bar wa Allah ne.

Saboda haka biyan diyyar na da kyau amma idan za a yi adalci.

Idan diyya ce ta ’yan SARS, ni na san suna musguna wa mutane, domin a cikin Fulaninmu mutanen da muke nema wadanda aka kama sun fi mutum 500.

Jami’an tsaron nan suna zuwa kasuwa su kama ’ya’yan Fulani su tafi da su, ba a san su wane ne suka kama su ba, ba a san ina ne aka kai su ba, shi ke nan sun bata.

Sai ka ga Bafulatani ya fita da babur, ya tafi kasuwa bai dawo ba; A je duk inda jami’an tsaro suke, su ce babu shi, saboda an kama shi ba tare da ka’ida ba.

 

Karshe mene ne sakonka ga gwamnati game da wannan al’amari?

Abin da zan ce shi ne, ina bakin cikin yadda Shugaban Kungiyar Neman Kafa Kasar Biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya fito yana fadin kalaman tayar da hankali kan wannan zanga-zanga.

An ji shi yana turo miyagun maganganu ta gidan rediyonsu na Biyafra daga kasar da yake zaune wato Ingila.

A cikin miyagun kalaman nasa yana cewa a kashe jami’an tsaro da shugabanni da manyan ’yan siyasar Najeriya.

Irin wannan dan ta’adda wanda tuni gwamnati ta haramta kungiyarsa, a ce ya tafi kasar Ingila ya zauna yana yin irin wadannan miyagun maganganu na tayar da hankali, ba daidai ba ne.

Don haka ina rokon Gwamnatin Tarayya ta gaya wa Ingila ta ba da wannan mutum ya zo Najeriya ya fuskanci hukunci.

Domin kashi 50 cikin 100 na barnar da aka yi, a wannan zanga-zanga shi ne ya yi sanadi.

Kuma ina rokon Gwamnatin Tarayya ta rika karbar shawarwarin da ake ba ta.

Domin abin bakin ciki ne, a ce manyan shugabannin kasar nan, suna ta bai wa wannan gwamnati shawara, amma ba ta sauraron su, balle ta rika zama da su, don su rika ba ta shawarwari.

Ya kamata ta daina sauraron ’yan barandarta, ta rika sauraron shawarwarin da ake ba ta.