#EndSARS: An sassauta dokar hana fita a Ebonyi
Gwamnatin jihar Ebonyi ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a jihar bayan tabbatar da harkokin jama’ar jihar sun daidaita.
Gwamnan Jihar Ebonyi Mista David Umahi
Gwamnatin Jihar Ebonyi ta sassauta dokar hana fita da ta kakaba ta sa’o’i 24 don tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar #ENDSARS da aka yi a jihar.
Daga ranar Juma’a mutane a jihar za su kasance a gidajensu daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 8:00 na safe.
- Yadda jawabin Buhari kan #EndSARS ya tayar da kura
- Kasashe sun ba mu Dala 400,000 —Masu Zanga-zangar #EndSARS
- #EndSARS: Ba za mu zura wa mabarnata ido ba —Buhari
Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya bukaci mahukunta da hukummin tsaro da kuma ’yan jihar su yi kokarin kiyaye doka a matsayin ’yan kasa masu kishi da kuma kauce wa duk wani abu da zai iya janyo rikici a zanga-zangar wanda ka iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar.
An sassauta dokar ne bayan kwana biyu yayin da wasu matasa suka yi yunkurin tayar da rikici lokacin zanga-zangar a wasu yankunan jihar.
Aminiya ta gano cewa, a yanzu haka an samu zaman lafiya a Abakiliki babban birnin jihar da kewaye.
An kuma bude shaguna sannan masu matocin sufuri da wasu cibiyoyi suna ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.