#EndSARS: Falz ya kaurace wa taron gwamnati

Shahararren mawakin Najeriya, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz ya janye halartar taron da Gwamnatin Tarayya ta shirya ta bidiyo domin kawo karshen zanga-zangar #EndSARS. Karfe 3 na ranar Jama’a za a fara taron da Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa ta kira wanda Falz ke daga cikin masu jawabi. Jama’a na da ’yancin […]

#EndSARS: Falz ya kaurace wa taron gwamnati

Mawaki n Najeriya Folari Falana wanda aka fi sani da Falz

Shahararren mawakin Najeriya, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz ya janye halartar taron da Gwamnatin Tarayya ta shirya ta bidiyo domin kawo karshen zanga-zangar #EndSARS.

Karfe 3 na ranar Jama’a za a fara taron da Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa ta kira wanda Falz ke daga cikin masu jawabi.

“Ban amince in zama daga cikin masu yawabi ba. Bayanan bogi aka ba ni kuma babu bukatar taron.

“Abin bukata kawai shi ne #5for5 #SARSMUSTEND”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Jama’ar.

Da farko taron ya gayyato Falz; Shugaba ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu; jagoran zanga-zangar #EndSARS, Segun Awosanya; da Jami’in DAI a Najeria, Joe Abah a matsayin masu jawabi a taron.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

Tags