#EndSARS: Kwamandan ’yan sanda ya tsallake rijiya da baya

Wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda ya tsallake rijiya da baya bayan masu zanga-zangar neman rushe ’yan sandan SARS sun yi kansa da mota. Kwamandan yankin Ajah a Legas, ACP Olugbemi Gbolahan ya sha da kyar ne a lokacin da wata ta kuskure shi amma ta bar shi da rauni a kafa. Kotu ta soke daukar […]

#EndSARS: Kwamandan ’yan sanda ya tsallake rijiya da baya

Zanga-zangar #EndSARS

Wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda ya tsallake rijiya da baya bayan masu zanga-zangar neman rushe ’yan sandan SARS sun yi kansa da mota.

Kwamandan yankin Ajah a Legas, ACP Olugbemi Gbolahan ya sha da kyar ne a lokacin da wata ta kuskure shi amma ta bar shi da rauni a kafa.

“Kwamandan Yankin ya halarci wurin domin gane wa kansa abin da ke faruwa da kuma tabbatar da tsaro ne a lokacin da mai motar ya yi tukin gangancin har ya kade shi.

“Ana jinyar sa a wani asibiti da ke yankin Ajah, Jihar Legas muna kuma kira ga masu znaga-zanga su kasance cikin nutsuwa da bin doka tare da yin abin da ya dace a koyaushe”, inji shi kakakin ’yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi.

Jami’in ya ce ACP Gbolahan ya gamu da gamonsa ne ne a daidai lokacin da mai zanga-zangar ke tukin ganganci yana layi da motar a kan hanya.

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo