Aminiyar KurmiHotuna• Created October 16, 2020 19:33
#EndSARS: Masu zanga zanga sun rufe manyan hanyoyin birnin Abeokuta
An gangi jami’an tsaro jefi-jefi da ke jiran tabbatar da kwantar da koda ta kwana.
Daruruwan matasa da ‘yan makaranta gami da masu hidimar kasa ta NYSC ne suka fito zanga zangar kin jinin ‘yan sandan SARS tun da safiyar Juma’a a Abeokuta.
Masu zanga zangan sun rufe hanyar zuwa ofishin gwamnatin jihar Ogun dake Oke Moson daga sashen babban gidan mai na NNPC da ke birnin Abeokuta, hanyar da ta hade birnin Abeokuta da garin shagamu da jihar Legas, lamarin da ya sanya tarin direbobi da fasinjoji yin curko-curko a kan hanya.
Zangan-zangar na ci gaba da gudana cikin salama inda aka hangi jami’an tsaro jefi jefi da ke jiran tabbatar da kwantar da koda ta kwana.
Wakilin Aminiya, Abbas Dalibi, ya kawo muku hotunan yadda zanga zangar ta rika gudana a Abeokuta.
Dandanzon matasa da suka rufe shataletatalen NNPC a kwaryar Birnin Abeokuta, hanyar da ta hade birnin da garin Shagamu, da Legas
Masu zanga zangar inda wasun su suka hau saman kantar da ‘yan sanda masu bada hannu ke amfani da ita
Wani sashe na masu zanga zanga
wani sashen masu zanga zangar a karkashin gada
Dandanzon ababan hawa da aka rufe wa hanya
Wani sashe na dandazon ababan hawa da aka hana masu wucewa
Matafiya da direbobin manyan motoci sun yi curkocurko
Wani sashe na direbobin manyan motoci da aka hana su shigewa
Wani sashe na direbobin a zazzaune akan hanya wadanda suka shaida wa Aminiya cewa sun shafe sama da awa shida suna zaune sakamakon rufe hanyarsu ta zuwa Legas da masu zanga zangar su kayi