Aminiyar KurmiHotuna• Created October 25, 2020 22:28
#EndSARS: Ministoci da gwamnonin Kudu sun ziyarci Legas
Sun alakanta ibtila’in da wani shiryayyen lamari da aka kitsa domin karya tattalin arzikin jihar.
A ranar Lahadi 25 ga watan Oktoban 2020 ne Ministoci da Gwamnonin yankin Kudu maso Yamma suka ziyarci Jihar Legas domin jajanta wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu kan dimbin asarar da zanga-zangar #EndSARS ta haifar a jihar.
Bayan da suka kewaya don gane wa idanunsu irin barnar da ta biyo bayan kone-konen, shugabannin sun yi zargin wani shiryayyen lamari ne da aka kitsa domin karya tattalin arzikin jihar Legas.
Wanda ya yi magana a madadinsu, Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana haka a lokacin ziyarar tasu.
Aminiya ta kawo maku hotunan ziyarar jajen da kuma gani da ido da shugabannin yankin suka kai jihar Legas.
Gwamnoni da ministocoin jihohin Kudu maso Yamma a lokacin ziyarar gane wa idanunsu barnar da rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar #EndSARS ya yi a Legas
Daga tsakiya, Ministan Ayyuka kuma tsohon Gwamnan Legas, Babatunde Fashola, sai Gwamnan Legas mai ci Babajide Sanwo-Olu a hagunsa, da kuma tsohon Gwamnan Osun kana Ministan Harkokin Cikin Gida, Ra’uf Arebgesola daga dama da shi sannan Gwamnan Oyo Seyi Makinde daga hagun gwamnan Legas
Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a lokacin da yake jawabi a madadin gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma a lokacin ziyarar jajen da suka kai a Legas
Tawagar gwamnonin suna duba irin barnar da tarzomar ta yi.
Sashen gwamnonin da ministocin a lokacin da suke gane wa idanunsu barnar da tarzomar ta haifar a Legas.
Wani sashe na gwamnonin da ministocin a lokacin rangadin gani da idon.
Tawagar gwamnonin da ministoci a lokacin da suka isa Lekki Toll Gate inda sashin zanga-zangar suka yi dandanzo ake kuma zargin sojoji sun yi harbi a kansu daren Talata
Gwamnonin da ministocin a lokacin da suke gane wa idanunsu barnar da tarzomar ta haddasa.