Enyeama zai fafata a Gasar Gwarzon ’Yan kwallon Afirka a Faransa
Golan Najeriya bincent Enyeama na daya daga cikin ’yan kwallon da za su fafata a Gasar Gwarzon ’Yan kwallon Afirka da ke Faransa. Gasar da ake wa lakabi da bibien Fo’e ta samo asali ne tun cikin shekarar 2009.Ana gudanar da gasar ce a duk shekara ga ’yan kwallon Afirka da ke wasa a gasar […]
Golan Najeriya bincent Enyeama na daya daga cikin ’yan kwallon da za su fafata a Gasar Gwarzon ’Yan kwallon Afirka da ke Faransa.
Gasar da ake wa lakabi da bibien Fo’e ta samo asali ne tun cikin shekarar 2009.
Ana gudanar da gasar ce a duk shekara ga ’yan kwallon Afirka da ke wasa a gasar rukuni-rukunin Faransa (Ligue 1) kuma gidajen rediyo da natalabijin mallakar suke gudanar da zaben.
bincent Enyeama ne ya lashe gasar a bara kuma yana daga cikin wadanda suke gaba-gaba da ake ganin za su iya lashe gasar a karo na biyu a bana.
An fito da gasar ce a shekarar 2009 bayan dan kwallon Kamaru Foe ya yanke jiki ya fadi a lokacin da wasa ke gudana a ranar 20 ga Yunin 2003 a lokacin da Kamaru take fafatawa a wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal) da Kolombiya a gasar cin kofin Confederation (FIFA Confederations Cup).
Baya ga Enyeama da ya lashe gasar a bara, sauran ’yan kwallon da suka taba lashewa sun hada da Maroune Chamakh (2009) da Gerrbinho da ya lashe a shekarun 2010 da 2011 da Younes Belland wanda ya lashe a shekarar 2012 da kuma Pierre-Emerick Aubameyang a shekarar 2013.