Erdogan ya ki yarda da bukatar Amurka
A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasar Turkiyya, Malam Recep Tayyip Erdogan ya mayar wa mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan Harkokin Waje, Mista John Bolton martani kan bukatar Turkiyya ta tabbatar da cewa ba za ta kai wa mayakan Kurdawa da ke Arewa maso Gabashin Siriya hari ba, kafin Amurka ta janye sojojinta daga kasar. […]
A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasar Turkiyya, Malam Recep Tayyip Erdogan ya mayar wa mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan Harkokin Waje, Mista John Bolton martani kan bukatar Turkiyya ta tabbatar da cewa ba za ta kai wa mayakan Kurdawa da ke Arewa maso Gabashin Siriya hari ba, kafin Amurka ta janye sojojinta daga kasar.
Shugaba Erdogan ya yi wannan kalami ne yayin da Mista Bolton ya kai ziyara Ankara babban birnin Turkiyya domin tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar. Erdogan ya soke ganawar da aka shirya zai yi da Bolton, maimakon haka sai Bolton ya gana da wasu jami’an gwamnati ciki har da mai magana da yawun Shugaban Kasar da kuma Ministan Tsaron Turkiyya.
Da yake magana a gaban mambobin jam’iyyarsa ta AK cikin kakkausar muryar, Erdogan ya yi watsi da maganar Bolton, yana mai cewa Turkiyya ba za ta amince da yin sulhu ba, yana mai danganta Kurdawan da sauran kungiyoyin ta’addanci a Siriya.
Shugaba Erdogan ya ce, “Akan wannan batu, John Bolton ya tafka babban kuskure, kuma duk wanda yake tunani irin wannan shi ma ya yi kuskure. Ba abu ne mai yiwuwa a wannan lokaci mu amince da wani sulhu ba. Duk wadanda ke cikin ’yan ta’adda a Siriya za su fuskanci darasin da ya dace da su. Babu wani bambanci a tsakanin ’yan kungiyar PKK da YPG da PYD da kuma Daesh.”
Bolton dai bai samu hadin kai ba a kokarin da ya shafe sa’o’i biyu yana yi domin neman sasantawa don kare Kurdawan da Amurka ke mara wa baya a Arewa maso Gabashin Siriya.