Erik Ten Hag zai ci gaba da zama a Manchester United
Ten Hag zai ƙulla sabuwar yarjejeniya da Manchester United.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, ta bayyana cewar kocinta Erik Ten Hag zai ci gaba da jan ragamar horar da ‘yan wasan ƙungiyar.
Wannan na cikin wata sanarwar, wadda ta ce ƙungiyar na kan tattaunawa da Ten Hag, kan tsawaita kwantaraginsa.
- HOTUNA: Yadda aka gudanar da bikin Ranar Dimokuradiyyar Najeriya
- Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar mataimakin shugaban ƙasar Malawi
An jima ana alaƙanta ƙungiyar da cewar za ta sallami kocin nata, amma bayan ya lashe kofin FA sai mahukuntan ƙungiyar suka sauya shawara kan sallamarsa.
Gabanin wasan karshe na kofin FA, wanda United ta buga da Manchester City a filin wasa na Wembley, an yi ta rade-radin cewa kungiyar za ta raba gari da Ten Hag, da zarar an kamala gasar.
Sai dai, nasarar da United ta samu da ci 2-1 ya bai wa shugabannin hukumar gudanarwar ƙungiyar damar fara tattauna makomar ƙungiyar cikin kyakkyawan yanayi.
Masu fashin baƙi kan harkar tamola irin su Fabrizio Romana, sun bayyana cewar Manchester United a baya ta yi tunanin fara zawarcin masu horarswa irin su Thomas Tuchel, Roberto De Zerbi da kuma Mauricio Pochettino wanda ya raba gari da Chelsea a baya-bayan nan.
A gefe guda an kuma alaƙanta ƙungiyar da mai horas da tawagar ’yan wasan Ingila, Gareth Southgate, amma daga ƙarshe Manchester United ta yanke hukuncin ci gaba da zama da Ten Hag.
Ana sa ran kocin zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar da zai ci gaba da zama a ƙungiyar na tsawon wasu shekaru.