Esther Hamisu: Burina mata su shiga siyasa gadan-gadan
Esther Hamisu Lauya ce kuma ‘yar siyasa. Ta rike mukamin shugabar matan Jam’iyyar CPC da APC na Jihar Gombe. Ta kasance mai fadi-tashin don mata su shiga harkar siyasa gadan-gadan, har su rika fitowa takara. Ta ba iyaye shawara a kan su ba ‘ya’yansu ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya. Tarihin rayuwataSunana Esther Hamisu, […]
Esther Hamisu Lauya ce kuma ‘yar siyasa. Ta rike mukamin shugabar matan Jam’iyyar CPC da APC na Jihar Gombe. Ta kasance mai fadi-tashin don mata su shiga harkar siyasa gadan-gadan, har su rika fitowa takara. Ta ba iyaye shawara a kan su ba ‘ya’yansu ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya.
Tarihin rayuwata
Sunana Esther Hamisu, ni kabilar Tula ce (Tula Wange) daga yankin karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe. An haife ni a garin Tula a ranar 27 ga watan Satumba, 1977. Na girma a garin Bauchi domin lokacin Gombe na karkashin Jihar Bauchi. A shekarar 1988 ne iyayena suka sanya ni a makarantar Firamare ta Nasarawa da ke karamar Hukumar Kaltungo, inda na kammala a shekarar 1995.
Daga nan sai na tafi Kwalejin Koyarwa ta ‘Yan mata da ke garin Kaltungo (WTC Kaltungo), ban gama ba aka cire ni aka mayar da ni Kwalejin kere-kere ta garin Tula (bocational Training Centre). A nan na kammala ajin karamar sakandare, sannan sai na tafi Babbar Sakandaren Gwamnati ta deke a karamar Hukumar Gwagwalada, Abuja. A nan kammala sakandare dina. Bayan na kammala ne sai na yi karamar Difloma a Makarantar Koyon Aikin Shari’a da ke garin Yola, Jihar Adamawa. Na ci gaba da karatu a makarantar har na samu shaidar Babbar Difloma. Bayan na kammala ban yi aikin gwamnati ba sai na shiga harkokin siyasa gadan-gadan, domin in kwato wa mata ’yanci a siyasance, saboda ganin komai ake yi a kasar nan an bar mata a baya sosai musammam ma a nan Jiharmu ta Gombe.
Dalilin da ya sa na shiga siyasa
Na shiga siyasa ne saboda ina son jama’a su samu ’yanci musammam ’yan uwana mata da aka bar su a baya. Na yi hakan don in jawo hankalinsu su shiga siyasa, su san abin da yake faruwa a jiha da ma kasa baki daya, kasancewar ana yin abubuwa da yawa ba a sa mata a ciki, tun da aka fara siyasa a kasar nan ba a taba samun mace ta zama Shugabar kasa ba, haka a Jihar Gombe kuma ba a taba samun mace ta zama gwamna ko mataimakiyar gwamna ba, sai dai a nada su kwamishinoni, hatta Manyan Sakatarorin Gwamnati ma (Permanent Secretary) a yanzu da wuya a samu mata biyu a Jihar Gombe. Ba wani abu ya kawo haka ba illa fifiko da mazaje suke nuna wa mata, inda maza ke yin kakagida sai lokacin zabe ya yi sai a rika yi musu zakin baki, a rika ce musu su fito su yi zabe bayan an danne su, sau daya aka taba samun mace ta zama Shugabar karamar Hukuma a karamar Hukumar Kaltungo, wato Hajiya Bibiye Abubakar Sadik, ta taba zama a lokacin mulkin tsohon Gwamna Abubukar Hashidu a karkashin Jam’iyyar APP. A zamanin Gwamna danjuma Goje kuma aka samu mata biyu suka zama ‘yan Majalisun Dokoki na jihar, amma yanzu al’amarin ya koma baya ko mace daya babu a zauren tsara dokokin da sunan ‘yar majalisa.
kalubale
Na fuskanci babban kalubale saboda na lura a kullum maza ba sa barin mata su yi katabus a harkokin siyasa, komai sai maza, kuma a gaskiya hakan da suke yi ba daidai ba ne, kuma ba zai bar mace ta samu ‘yancin da take nema ba, dole ne sai an bar mata sun fito sun taka rawar gani an kuma dama da su sosai, kafin komai ya tafi daidai. Ni ma da kake gani yanzu haka a baya ni ce tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar CPC da aka yi hadaka aka zama APC ma ni ce shugabar mata, amma yanzu an sauke mu sai bayan mun gudanar da babban taron jam’iyya na kasa, kafin a sake zaben shugabannin jam’iyyar.
Nasarorin da na samu
Wato ita Nasara a siyasance ko kuwa a sha’anin rayuwa abu ne da kwazonka ne zai samar maka da ita, lailai babu shakka a tafiyarmu ta siyasa na samu babbar nasara, domin a siyasa wadanda muke fada da su a lokacin da suke jam’iyya mai mulki ni ina jam’iyyar adawa yanzu duk na samu shawo kansu mun dawo jam’iyya daya ta adawa, wanda za mu hadu mu yaki jam’iyya mai ci, kuma wadannan mutane su ne irin su Sanata danjuma Goje da Usman Bayero Nafada da Inuwa Yahaya da Abubakar Aliyu da sauransu, sannan kuma a jam’iyyar adawar na yi kokari na kawo ‘yan majalisun dokoki guda hudu daga jam’iyyarmu ta adawa ta CPC, wanda yanzu ita ce APC sannan na kawo dan majalisar tarayya daya a zaben gama-gari na shekarar 2011 da ya gabata.
Burina a siyasa
Burina a siyasa shi ne idan maza sun ba wa mata dama su fara fitowa sosai ana damawa da su a siyasa, nan gaba idan muka kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP jam’iyyarmu ta kafa gwamnati, to burina in nemi takarar gwamna don in ceto Jiharmu, in kuma ba mata ‘’yancinsu a siyasance.
Abin da ya fi burge ni a rayuwa
A gaskiya ni ‘yar siyasa ce amma abin da ya fi burge ni shi ne, in ga mutum ya rike amana. Yana kwantanta gaskiya da kuma cika alkawari.
Shawarata ga mata
Ina ba iyaye mata shawarar komai rintsi abar ‘ya mace ta yi ilimi na zamani da kuma addini, domin ilimi shi ne gishirin rayuwa, idan aka ce maka yau mace ba ta yi karatu to za a samu matsala, saboda babu yadda al’amuranta za su tafi daidai da wacce ta yi karatu, duk da cewa wasu na ganin ilimi shi ke sa mace tsabta da tarbiya ba haka ba ne, ilimi da tarbiya duk tafiyarsu daban-daban ne, amma dai wata mai ilimin tana iya samunsu duka fiye da wacce ba ta da shi, sannan kuma idan mace ta yi karatu tana iya amfanar duk zuri’arta da ribar wannan karatun ga tausayin iyaye fiye da da namiji, don haka iyaye abar mata su yi ilimin zamani, a kuma kiyaye dora wa ‘ya’ya mata talla, saboda talla na gurbata tarbiya kwarai da gaske, domin a wurin talla ne kawai ‘ya mace za ta iya cudanya da kowanne irin da namiji nagari da na banza, wasu iyayen ma idan sun dora wa ‘yarsu talla sukan ba ta lasisin lalacewa, domin cewa suke yi kada ta yarda ta dawo musu da kwashe.
wanda yanzu ita ce APC sannan na kawo dan majalisar tarayya daya a zaben gama-gari na shekarar 2011 da ya gabata.
Burina a siyasa
Burina a siyasa shi ne idan maza sun ba wa mata dama su fara fitowa sosai ana damawa da su a siyasa, nan gaba idan muka kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP jam’iyyarmu ta kafa gwamnati, to burina in nemi takarar gwamna don in ceto Jiharmu, in kuma ba mata ‘’yancinsu a siyasance.
Abin da ya fi burge ni a rayuwa
A gaskiya ni ‘yar siyasa ce amma abin da ya fi burge ni shi ne, in ga mutum ya rike amana. Yana kwantanta gaskiya da kuma cika alkawari.
Shawarata ga mata
Ina ba iyaye mata shawarar komai rintsi abar ‘ya mace ta yi ilimi na zamani da kuma addini, domin ilimi shi ne gishirin rayuwa, idan aka ce maka yau mace ba ta yi karatu to za a samu matsala, saboda babu yadda al’amuranta za su tafi daidai da wacce ta yi karatu, duk da cewa wasu na ganin ilimi shi ke sa mace tsabta da tarbiya ba haka ba ne, ilimi da tarbiya duk tafiyarsu daban-daban ne, amma dai wata mai ilimin tana iya samunsu duka fiye da wacce ba ta da shi, sannan kuma idan mace ta yi karatu tana iya amfanar duk zuri’arta da ribar wannan karatun ga tausayin iyaye fiye da da namiji.
don haka iyaye abar mata su yi ilimin zamani, a kuma kiyaye dora wa ‘ya’ya mata talla, saboda talla na gurbata tarbiya kwarai da gaske, domin a wurin talla ne kawai ‘ya mace za ta iya cudanya da kowanne irin da namiji nagari da na banza, wasu iyayen ma idan sun dora wa ‘yarsu talla sukan ba ta lasisin lalacewa, domin cewa suke yi kada ta yarda ta dawo musu da kwashe.