Etsun Nupe ne Amirul Hajjin bana

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana Etsun Nupe Alhaji Yahaya Abubakar a matsayin Amirul Hajjin bana da zai jagoranci alhazan Najeriya daga nan zuwa kasa Mai tsarki.Sarkin Musulmin ya ce “Duk da Gwamnatin Tarayya ba ta ayyana Amirul Hajji ba a matsayimu na jagororin Musulmi mun zauna mun tattauna mun ga ya […]

Etsun Nupe ne Amirul Hajjin bana
Etsun Nupe ne Amirul Hajjin bana

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana Etsun Nupe Alhaji Yahaya Abubakar a matsayin Amirul Hajjin bana da zai jagoranci alhazan Najeriya daga nan zuwa kasa Mai tsarki.
Sarkin Musulmin ya ce “Duk da Gwamnatin Tarayya ba ta ayyana Amirul Hajji ba a matsayimu na jagororin Musulmi mun zauna mun tattauna mun ga ya dace a nada wanda zai jagorancin jama’armu a kasa Mai tsarki domin Musulmi ba su tafiya ba shugaba, kan haka muka umarci Etsu Nupe ya jagoranci mahajjatanmu a aikin Hajjin bana.
Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata a wajen bikin kaddamar da tashin maniyyatan bana da aka fara da mahajjatan Jihar Zamfara, inda ya bukaci maniyyatan su ji tsoron Allah a yayin zamansu a kasa Mai tsarki kuma su yi wa kasa da jagororinta addu’ar alheri.
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wanda shi ne ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi addu’a ga alhazan da suka rasu a tirmitsitsin da aka samu a Hajjin bara, kuma ya nemi wadanda za su tafi a bana su yi wa kasa addu’a da wadanda suka rasu a can kuma su zama jakadu nagari da za su kare martabar kasa da addininsu.
Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da Amirul Hajjin Etsu Nupe a jawabansu sun yi kira ga alhazai su mayar da hankali ga abin da suka je yi, su guji duk wani abu mara kyau ko aikin assha a lokacin aikin Hajjin kuma su kiyaye dokokin kasar Saudiyya.    
Shugaban Hukumar Hajji ta kasa Alhaji Abdullahi Mukhtar, ya ce za a kwashe mahajjatan Najeriya dubu 65 da 500 wadanda dubu 57 suka biya kudin kujera ta hannun hukumomin alhazai na jihohi da ta kasa yayin da 8,500 suka biya ta hannun kamfanoni masu zaman kansu. Ya ce sun tsara jigilar za a yi sawu 130 a karkashin kulawar kwamitoci 52 a Nkjeriya da Saudiyya.
Alhaji Abdullahi Mukhtar ya ce “Tsarin canja wa maniyyata Dala a kan Naira 197 ba an dage musu kafa ba ne a kan tsarin da gwamnati ta fito da shi na janye hannunta kan hada-hadar kudi sai dai alkawari ne aka cika domin mun rubata wa gwamnati tun a watan Maris na bara muna bukatar ta ba mu farashin Dala a kan haka, kuma ta amince za ta yi, ya kamata mutane su sani wannan tsohuwar magana ce saboda ba a fara tsara aikin Hajji lokaci guda, bata suna ne da maganganu marasa tushe a rika yada cewa gwamnatin Najeriya ta dage wa  maniyyata kafa wajen musayar,” inji shi.
Ya ce sun yi tsari mai kyau a kasa Mai tsarki musamman kan kiwon lafiya inda suka fito da wasu na’urori na ajiye kwayoyin halitta da suke diba a bakin mahajjaci kafin ya shiga jirgi su adana don bacin rana da ba su fata. Kuma ya ce sun tanadi wurare masu kyau kusa ga harami a Makka da Madina kuma akwai shiri na bayar da abinci kyauta, bayan kowane Alhaji an ba shi wata na’ura kamar agogo da zai sanya a hannu da za ta taimake shi duk lokacin da ya shiga matsala.
Maniyyata 493 suka tashi a jirgin farko wadanda suka fito daga kananan hukumomin Bukuyum da Maradun yayin da aka saukar da bakwai daga cikinsu mata biyar da maza biyu kan rashin takardar shiga jirgin.