EU na nazarin hana yara amfani da kafafen sada zumunta

EU na ci gaba da matsa wa kamfanonin Facebook, Instagram da TikTok lamba su sauya wasu tsare-tsarensu.

EU na nazarin hana yara amfani da kafafen sada zumunta

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta soma nazari kan yiwuwar hana yara amfani da kafafen sada zumunta domin kare su daga illolin da ke intanet.

A wannan Litinin din ce kwamitin ƙwararru da ya ƙunshi likitoci, da masana, da wakilan matasa da kuma iyaye ya gabatar da shawarwarinsa.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta nuna goyon bayan hana yara shiga kafafen sada zumunta, kuma ana sa ran za a gabatar da wata doka kan ƙayyade shekarun masu amfani da kafofin a wannan bazarar.

A lokaci guda, EU na ƙara matsa wa kamfanonin Facebook, da Instagram da TikTok lamba, su sauya tsarin wasu abubuwan da ake wallafawa da ake ganin suna haddasa munanan dabi’u da ake amfani da su a kafafen sada zumunta.