EU ta dauki matakin shari’a na kakaba wa Nijar takunkumi
EU ta aika saƙo ƙarara cewa akwai hukuncin da ke zuwa bayan juyin mulkin soja.
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta dauki matakin shari’a domin kakaba takunkumi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Tarayyar ta Turai mai kasashe 27 ta yi Allah wadai da hambarar da gwamnatin zababben shugaban Nijar Mohamed Bazoum.
- Google na bikin cika shekaru 60 da haihuwar marigayi Rashidi Yekini
- Najeriya ta yi galaba kan kamfanin P&ID a shari’ar bashin dala biliyan 11
Tarayyar Turan ta dauki matakai na shari’a inda a halin yanzu za ta iya saka “takunkumi kan jama’a ko kamfanoni wadanda suke da alhakin kawo barazana ga tsaro ko zaman lafiya kan Nijar,” kamar yadda ta bayyana a ranar Litinin.
Shugaban tsare-tsaren harkokin waje na tarayyar ya bayyana cewa wannan matakin “zai aika sako cewa akwai matakin da ke biyo bayan juyin mulkin soji.
Kungiyar ta kuma ce takunkumin zai shafi mutanen da ke zagon ƙasa ga tsarin mulkin Nijar da dimokraɗiyya ko bin doka, da kuma mutanen da ke keta haƙƙin bil’adama ko cin zarafi.
Takunkuman za su haɗa da hana tafiye-tafiye da rufe kadarori da kuma hana ba da kuɗaɗe ga mutanen da aka sanyawa takunkuman.
” Da wannan shawara da ta yanke a yau, tarayyar EU ta ƙarfafa goyon bayanta ga ƙoƙarin ƙungiyar ECOWAS, kuma ta aike da saƙo ƙarara cewa akwai hukuncin da ke zuwa bayan juyin mulkin soja,” in ji babban jami’in harkokin wajen EU Josep Borrell.
Tuni Tarayyar Turai ta dakatar da hadin kan tsaro da kuma tallafin kudi ga Nijar bayan sojoji sun kwace mulkin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Daina bayar da tallafi
“Matakan da aka dauka sun hada da kwace kadarori da kuma hana bayar da kudi ga jama’a da kuma kamfanoni, da kuma haramta tafiye-tafiye ga jama’a,” kamar yadda Turai ta ce a wata sanarwa.
Kasar da ta yi wa Nijar mulkin-mallaka wato Faransa a halin yanzu tana janye dakarunta 1,500 daga kasar bayan sojojin na Nijar sun bukaci hakan.
Kasashen Yamma na kallon hambarar da Bazoum a matsayin wani babban koma- baya a yakin da suke yi da ta’addanci a yankin Sahel saboda ana kallon Bazoum a matsayin babban mai bayar da gudunmawa.
Kungiyar ECOWAS ta saka takunkumi kan kasar a daidai lokacin da ake juyin mulki a yankin na Sahel. Sai dai a halin yanzu tana bin hanyoyin diflomasiyya domin magance lamarin.