EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno

EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon shekaru goma.

EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi.

EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma.

Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna.

Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da ganin irin damar da cibiyar sana’ar ta ke ba wa al’ummar jihar Borno da ma sauran su.

Ya ce, “Ina yabawa da wannan gagarumin nasara misali ɗaya ne na cibiyoyi da dama da gwamnatin jihar ta gina a ƙarƙashin jagorancin gwamna Zulum da hangen nesansa.

“Koyar da sana’o’i a bayyane yake – abu ne da matasa a jihar ke buƙata, kuma wannan wani abu ne da muka samu a Turai, musamman a Jamus.

“Mun yi nazari kan tarin ayyukan da taimakon jin kai da haɓaka haɗin gwiwa a fannoni da dama da Gwamnan ya aiwatar a Jihar Borno.

“Jihar Borno za ta kasance wani muhimmin yanki na haɗin gwiwar Turai a cikin shekaru masu zuwa.

Wakilin Jakadan Jamus, Karen Jensen, ya yaba wa Gwamna Zulum bisa yadda ya bai wa mata dama ta kowace fuska na rayuwa.

Jensen ya bayyana jin daɗinsa game da yawan mata da ke halartar shirye-shiryen koyar da sana’o’i daban-daban a cibiyar, musamman a fannonin da maza suka fi rinjaye kamar walda, tana mai cewa, “yana da muhimmanci mata su kasance sun samu ilimin sana’a.

“Ina alfahari da abin da nake gani a nan kuma aikin haɗin gwiwarmu yana da kyau sosai,” in ji Jensen.

Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ta je gidan gwamnati ne domin kai wa Gwamna Babagana Umara Zulum ziyara, inda Ƙungiyar Tarayyar Turai ta jaddada ƙudirinta na haɗa gwiwa da Gwamnatin Borno a ayyukan samar da zaman lafiya da hukumar haɗin kan kasa da kasa ta Jamus za ta aiwatar.

Da yake jawabi a wurin taron da ya gudana a Fadar Gwamnatin Borno, wakilin Hukumar Abinci da Aikin Noma na Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) a Nijeriya da ECOWAS, Koffy Dominique Kouacou, ya yaba da salon jagorancin Gwamna Zulum wajen bunƙasa noma da ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida ta hanyar kirkire-kirkire, samar da ababen more rayuwa da sauransu.

Ya ce za su yi aiki tare da Gwamnatin Zulum wajen gano hanyoyin da suka fi dacewa domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar ta hanyar inganta ayyukan noma, samar da tsarin abinci mai ɗorewa, da baiwa manoma da al’umma damar dogaro da kai.