EURO: Ingila ta kai wasan kusa da na ƙarshe

Ingila ta kai wasan kusa da na ƙarshe bayan doke Switzerland a bugun fenareti.

EURO: Ingila ta kai wasan kusa da na ƙarshe

Ƙasar Ingila ta kai wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Nahiyar Turai ta Euro da ake bugawa a ƙasar Jamus, bayan doke Switzerland a bugun fenareti.

Tun da farko dai ɗan wasan gaban Switzerland, Embolo ne ya fara jefa mata ƙwallo a minti na 75 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Shi kuwa Bukayo Saka, ɗan wasan gaban Ingila ta warware ƙwallon a minti na 80, lamarin da ya kai ƙasashen biyu kai ƙarin lokaci.

An yi kashin farko na ƙarin lokacin ba tare da kowa ya zura ƙwallo ba, lamarin da ya sa aka sake komawa kashi na biyu na ƙarin lokacin, wanda shi ma aka ƙare ba tare da an zura wa kowa ƙwallo ba.

Hakan ne ya sa aka tafi bugun taba gardama wato fenareti tsakanin ƙasashen biyu.

’Yan wasan Ingila baki ɗaya sun ci ƙwallayensu a bugun fenareti da aka yi, yayin da ɗan wasan bayan Switzerland, Manuel Akanji, wanda shi ne ya fara buga wa ƙasarsa fenareti ya zubar.

Hakan ya sanya aka tashi bugun fenaretin, Ingila na da ci 5, yayin da Switzerland ke da ci huɗu.

Ingila za ta kara da ɗaya daga cikin wanda ya yi nasara tsakanin Netherlands ko Turkiyya.