Everton ta kori Frank Lampard
Ana zargin tsohon kocin Wolves da Tottenham ne zai maye gurbin Lampard.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila ta yi hannun riga da kocinta, Frank Lampard.
Everton ta sallami Lampard ne bayan ‘mummunar’ rashin nasarar da ta yi a wasan Firimiyar Ingila da fafata da West Ham a karshen mako.
Kungiyar da ake yi wa lakabi da Toffees ta sha kashi da ci biyu da nema a filin wasa na Landan, wasan da aka yi hasashen shi zai raba gardamar zaman Lampard a matsayin kocin Everton.
Rashin nasarar dai ita cikon ta 9 da kungiyar ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a bayan nan
Da sakamakon wasan dai Everton ta koma ta 19 a teburin Firimiyar Ingila da zarar maki biyu tsakaninta da ta karshe a rukunin ukun karshe wadanda za su koma buga gasar ’yan dagaji muddin kakar wasannin ta kare suna wannan matsayi.
Goal ta ruwaito cewa, mai kungiyar Everton, Farhad Moshiri, wanda aka yi mamakin ganinsa cikin mahalarta kallon wasan da suka sha kashi, ya ce sallamar Lampard ba shawararsa ba ce, sai dai ya ce an yi ta ne bayan hukuncin da Majalisar Gudanarwa ta kungiyar ta zartar.
Lampard mai shekara 44 tsohon dan kwallon tawagar Ingila, wanda ya maye gurbin Rafael Benitez a Janairun 2022 a lokacin da kungiyar ke mataki na 16.
Ana dai rade-radin cewa tsohon kociyan Wolves da Tottenham, Nuno Espirito Santos ne zauna maye gurbin Lampard, duk da yake yana jan ragamar horas da ’yan wasan kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya.
Haka kuma, ana hasashen akwai yiwuwar tsohon kocin Burnley, Sean Dyche zai iya karbar ragamar horas da ’yan wasa a Everton, la’akari da cewa tun a karshen kakar da ta gabata ya rasa aikinsa.