Everton ta sallami Rafael Benitez

Everton ta bayar da tazarar maki shida tsakaninta da rukunin wadanda za a kora zuwa gasar ’yan dagaji.

Everton ta sallami Rafael Benitez

Rafael Benitez

Kungiyar Kwallon Kafa ta Everton ta raba gari da kocinta, Rafael Benitez bayan shafe watanni takwas yana jan ragamar horar da ’yan wasanta.

A watan Yunin bara ne dai Everton ta dauke shi a matsayin sabon kocinta, bayan ya shafe shekaru yana wannan aiki a Liverpool, wadda ta kasance daya daga cikin kungiyoyin da suke bakar hamayya da juna a Ingila.

Sallamar da Everton ta yi wa Benitez a ranar Lahadi na zuwa ne a sakamakon rashin katabus, inda a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 9 cikin 13 da ta buga a gasar Firimiyar Ingila ta bana.

Bayanai sun ce shan kashin da kungiyar ta yi a hannun Norwich City da ci 2-1 ranar Asabar ne ya kara rura wutar fatattakar Benitez ba tare da wani jinkiri ba.

Tun a wasan ne magoya bayan kungiyar Everton suka rika wake da kururuwar a sallami Benitez la’akari da yadda ya janyo musu abin kunya na rashin nasara a hannun Norwich City da suke gani karanta bai kai irin wannan tsaikon ba.

A yammacin jiya Asabar din ce kungiyar ta kira taron gaggawa inda ta tattauna a kan makomarsa, wanda aka rika rade-radin an fi bayar da rinjayen sallamarsa a taron.

Kafin yanzu, an dai rika ganin cewa dauko Benitez da mai kungiyar ta Everton, Farhad Moshiri ya yi babban kuskure ne wanda masu sharhi a kan wasannin kwallon kafa suka kira lamarin a matsayin caca da makomar kungiyar.

Benitez ya taba fusata magoya bayan Eveton yayin da ya bayyana kungiyar a matsayin ’yar kankanuwar kungiya a lokacin da yake aikin horaswa a Liverpool, kungiyar da ya jagoranra wajen samun nasara a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai da ta fafata da AC Milan a shekarar 2005.

A watan da ya gabata ne Moshori ya tsaya tsayin-daka wajen goyon bayan Benitez, inda ya bukaci a ba shi lokaci ya sauya al’amura a kungiyar idan ta sayi sabbin ’yan wasa sannan wadanda suke jinya suka warke.

Sai dai duk da haka, ba ta sauya zani ba a yayin da kungiyar ta ci gaba da rashin katabus da har ta kai ga hakurin magoya bayan kungiyar ya kai makura.

A yanzu da Benitez ya tattara komatsansa ya kama gabansa, kungiyar tana mataki na 16, inda ta bayar da tazarar maki shida kacal tsakaninta da rukunin wadanda za a kora zuwa buga gasar ’yan dagaji.