Eyimba ta sake lashe kofin kalubale a karo na hudu
kungiyar kwallon kafa ta Eyimba ta sake lashe kofin kalubale bayan da ta lallasa abokiyar hamayyarta ta Dolphins da ci biyu da daya a wasan karshen da suka buga a karshen makon da ya gabata a filin wasa na Teslim Balogun da ke Jihar Legas.Kulub din Eyimba da ke garin Aba wanda ya lashe kofin […]
kungiyar kwallon kafa ta Eyimba ta sake lashe kofin kalubale bayan da ta lallasa abokiyar hamayyarta ta Dolphins da ci biyu da daya a wasan karshen da suka buga a karshen makon da ya gabata a filin wasa na Teslim Balogun da ke Jihar Legas.
Kulub din Eyimba da ke garin Aba wanda ya lashe kofin kalubale a shekarar 2005 da 2009 da kuma 2013 ya kasance kulab na takwas da ya lashe gasar a jere.
Nasarar da kulab din ya samu za ta kwantar da hankulan shugabanni da ’yan wasa da masoya kulab din musamman idan aka yi la’akari da rashin nasarar da suka samu yayin haduwar su da kulob din Kano Pillers a gasar rukunin firimiya wacce kamfanin GLO ya shirya a kwanakin baya.
kungiyar Eyimba ta yi amfani da dukkan damar da ta samu yayin gasar a kan abokiyar hamayyarta wacce ita ma ba kanwar-lasa ba ce.
Duk da irin harin da suka rika kai wa juna da kuma kwararrun ’yan wasan da bangarorin biyu suka yi amfani da su ba a zura kwallo a raga ba sai bayan minti na 52 inda dan wasa Mfor Udoh na Eyimba ya zura kwallo ta farko a ragar Dolphins.
Bayan minti 20 kuma dan wasan Eyimba mai suna Chinonso Okonkwo ya zura kwallo ta biyu a ragar Dolphins bayan ba aka samu kuskure tsakanin mai tsaron gidan Dolphins da mai tsaron bayansa.
Amma duk da haka kungiyar Dolphins ba ta yi kasa a gwiwa ba domin kuwa sai da dan wasanta mai suna Enem Eduok ya zura kwallo a ragar Eyimba amma ina lokaci ya kurewa Dolphins ta fatakwal.
Saura kiris dan wasan Eyimba ya sake zura kwallo ta uku a ragar Dolphins ba don mai tsaron gidan kulab din mai suna Rotimi ya hana cin kwallayen da aka rika bugo masa ba yayin da ake kawo masa hare-hare.