FA za ta hukunta Ronaldo kan cin zarafin dan kallo

A watan Agusta kuma ’yan sanda suka ja wa Ronaldo kunne.

FA za ta hukunta Ronaldo kan cin zarafin dan kallo

Cristiano Ronaldo

Hukumar kwallon kafar Ingila FA ta daura damarar hukunta dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo kan cin zarafin wani dan kallo.

Wani hoton bidiyon da aka nada tun a watan Afrilun da ya gabata ya nuna dan wasan ya kwala wayar wani magoyin baya da kasa da ya yi kokarin daukarsa hoto.

Bidiyon wanda aka rika yadawa a kafafen sada zumunta an yi ikirarin cewa, ya buga wayar ne a kasa bayan fita daga filin wasa.

Wannan dai ta faru ne bayan kashin da United ta sha a hannun Everton da ci 1-0 a kakar wasanni ta bara.

Ronaldo mai shekara 37 daga baya ya nemi afuwar magoyin bayan a kafafen sada zumunta, har ya yi masa tayin zuwa yawon bude a filin wasa na Old Trafford.

Sai dai daga bisani mahaifiyar dan kallon ta yi watsi da tayin.

An ruwaito cewa, a watan Agusta kuma ’yan sanda suka ja masa kunne.

“An yi zargin halayyar da dan wasan gaban ya nuna bayan an tashi daga wasan ba ta dace ba,” in ji FA.

Manchester United ta ce za ta goyi bayan Ronaldo a matakin da zai dauka kan tuhumar.

A halin yanzu dai dan wasan yana tare da tawagar kasarsa ta Portugal, inda a ranar Asabar za su fafata ta tawagar Jamhuriyyar Czech da kuma Sfaniya bayan kwanaki biyu a gasar Nations League.

A farkon watan Oktoba ne dai za a buga wasa tsakanin Manchester United da Manchester City a gasar Firimiyar Ingila.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50