Faccala ta lakada wa faccalarta duka da itace a Kano

Ta dake ta da itacen ne saboda shara

Faccala ta lakada wa faccalarta duka da itace a Kano

An gurfanar da matar aure a Kotun Shariar Musulunci da ke cikin Hukumar Hisbah a Jihar Kano  bisa zarginta da laifin lakada wa faccalarta duka.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ASP Habu Muhammad, ya shaida wa kotun cewa wata mata mai suna Zainab Muhammad Sheka ce ta yi karar matar dan uwan mijin nata mai suna Maryam Dauda a gaban kotun.

Maryam ta yi zargin cewa Zainab ta yi mata duka da itace ta yi ta kwada mata shi a goshi lamarin da ya janyo samun rauni a goshinta.

Takardar karar ta kara da cewa wacce ake zargin ta doki mai karar ne sakamakon zargin da ta yi mata cewa ta watsa mata shara a kofar dakinta.

Sai dai wacce ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa na cin mutunci da gwada karfi da jin rauni.

Alkalin kotun, Mai Sharia Sani Tanimu Hausawa ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Agusta domin yanke hukunci.

Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah

Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira