Facebook da Instagram sun dawo aiki
Har ya zuwa yanzu ba a samu tabbacin dalilin afkuwar wannan lamari ba.
Shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram sun dawo aiki bayan tsayawa na tsawon wasu sa’o’i a wasu sassan duniya.
Tun da farko a wannan Talatar aka shiga ruɗani yayin da mutane suka kasa shiga shafukansu na Facebook da Instagram.
Masu amfani da shafukan Facebook da Instagram sun shiga ruɗani bayan da Kamfanin Meta — mamallakin shafukan sada zumuntar — ya gamu da tangarda a Yammacin ranar Talata.
Dubban ma’abota shafukan ne suka fara bayyana koke a yanar gizo yayin da masu amfani da Facebook, Messenger, da Instagram suka ruwaito cewa an kore su daga shafukansu ba tare da sanarwa ba.
Wannan lamari na gama-gari ya fara nunawa akan na’urorin mutane a Amurka, daga bisani kuma ya karade kusan ko’ina a faɗin duniya.
Da yawa daga waɗanda suka yi yunkurin shiga shafukansu sun farga da tangardar, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a intanet.
Da farko dai dubban masu amfani ne suka fara fuskantar matsalar, amma daga bisani cikin kankanin lokaci ta koma miliyoyi.
Duk wani kokari da masu amfani da shafukan suka yi don hawa zaurukan guda biyu ya ci tura, inda aka buɗe wani maudu’i a shafin X mai taken “Facebook and Instagram down” ma’ana Facebook da Instagram sun tsaya aiki.
Har ya zuwa yanzu ba a samu tabbacin dalilin afkuwar wannan lamari ba.
Sai dai mai magana da yawun Meta, Andy Stone, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ya bayyana cewa kamfanin yana sane da matsalolin da masu amfani da shafukan suka fuskanta.
“Muna sane da cewa mutane suna fuskantar matsala wajen shiga shafukanmu. Muna ƙoƙarin shawo kan matsalar a yanzu, ”in ji Stone.