Fada da ’yar sanda ya kai matashiya gidan yari

Kotu ta tisa keyar wata matashiya zuwa gidan yari saboda kai wa wata ’yar sanda hari a yankin A’jah da ke Jihar Legas.

Fada da ’yar sanda ya kai matashiya gidan yari

Kotu ta tisa keyar wata matashiya zuwa gidan yari saboda kai wa wata ’yar sanda hari a yankin A’jah da ke Jihar Legas.

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gurfanar da matar mai shekaru 26 ne bayan da kyamara kan titi ta kama ta tana cin zarafin wata ’yar sanda.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan ta ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu a shafinsa na X.

Hundeyin ya ce “Mun gurfanar da wata ’yar shekara 26 a gaban kuliya bisa mummunan hari da ta kai wa wata ’yar sanda, bayan da kyamara ta dauko hoton  cin zarafin a ranar 21 ga Fabrairu, 2024.

“Washegari aka gurfanar da ita a gaban kotun majistare ta Etiosa, Ajah, kuma an tasa keyarta zuwa gidan yarin Kirikiri har zuwa ranar zama na gaba, 27 ga Maris, 2024.

“Rundunar ‘’yan sandan tana kira ga jama’ar jihar Legas da su kasance masu bin doka da oda a harkokinsu na yau da kullum, domin duk wanda aka samu da laifin karya doka za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.”

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania