Fada ya kaure tsakanin jami’an tsaro a wurin rantsar da Gwamnan Kano
Dan sandan ya gaura wa jami’in immigration din mari a fuska, lamarin da ta janyo suka kaure da kokawa.
Fada ya kaure tsakanin wani jami’in Hukumar Shige da Fice ta Kasa (Immigration) da wani dan sanda a a wurin taron rantsar da zababben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam.
Lamarin ya auku ne a yayin da jami’an tsaron suke kokarin gyaran hanya ga motocin da zababben gwamnan da mataimakin nasa suke ciki don su samu shiga cikin filin taron.
- An hana Ganduje shiga wurin manyan baki a filin rantsar da Tinubu
- An jefi Sarkin Kano a filin rantsar da Abba Gida-Gida
Tunda farko lamarin ya fara ne da cacar baki a tsakaninsu, kafin daga bisani dan sandan ya gaura wa jami’in immigration din mari a fuska, lamarin da ta janyo suka kaure da kokawa.
Hakan ya janyo abokan aikin jami’in immigration din suka yi kan dan sanda har daya daga cikinsu yana kokarin yin harbi.
Sai da ta kai wasu jami’an yan sanda suka shiga tsakanin kafin al’amura su koma daidai.