Fadakarwa: Yau zabe saura kwana 57

Yau 21 ga Disamba 2018, a kidaya saura kwana 57 a yi zaben Shugaban Kasa, idan Allah Ya kai mu 16 ga Fabrairu, 2019. A yau GIZAGO (08065576011) tsokacinsa ya fadakar da al’ummar kasa ne dangane da zabe mai zuwa:   A matsayinka na dan Najeriya mai ’yanci da tsinkaye, ya kamata tun yanzu ka fara […]

Fadakarwa: Yau zabe saura kwana 57

Yau 21 ga Disamba 2018, a kidaya saura kwana 57 a yi zaben Shugaban Kasa, idan Allah Ya kai mu 16 ga Fabrairu, 2019. A yau GIZAGO (08065576011) tsokacinsa ya fadakar da al’ummar kasa ne dangane da zabe mai zuwa:

 

A matsayinka na dan Najeriya mai ’yanci da tsinkaye, ya kamata tun yanzu ka fara shirya tunaninka, domin yi wa kanka zabi nagari. To me ya kamata ka nazarta? Abu na farko da za ka saka a ranka shi ne, shin wane kudiri kake da shi ga kanka da kasarka? Wane dan takara ne zai iya taimaka maka domin cimma wannan buri naka? Don haka, kafin nan da kwanaki 57, ka tanadi amsoshin nan, domin yi wa kanka da kasarka zabin shugaban da ya dace.

Kamar yadda muka yi tambihi a sama, cewa shin mene kudirinka da na kasarka a yayin zaben shugaba? To, kafin ka ida gano bakin zaren, maza ka tsunduma cikin nazarin jam’iyyu da ’yan takarar da suke ta kai-komo domin ganin ka amince musu, ka zabe su yi maka shugabanci.

Shin mene kudiri da manufofin jam’iyyar da za ka zaba? Shin ta dace da manufofin gina kasa da gina al’umma? Idan ta dace, to tana da karfin halin aiwatar da su domin ci gaban kasa?

Shin mene ne manufa da kudirin dan takarar da kake son ka zaba? Domin kuwa ya kamata ka sani cewa, kowane dan Adam yana da manufa da dalilinsa na aikata wani abu.

Mutumin da za ka zaba, wane ne shi a rayuwarsa ta baya? Mai fada da cikawa ne, mai kishin kasa ne ko kuwa mai kishin kansa da gidansa ne kadai? Shin zai iya biyan bukatun kasa ko kuwa ba zai iya ba?

Wadannan tambayoyi tare da wasunsu, su ne abubuwan dubawa da nazari, kafin nan da kwanaki 57 masu zuwa, inda za a yi tungar zaben Shugaban Najeriya.

Ya kamata kuma mu mai da hankali game da wa’adin Shugaban Kasa, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada. A Najeriya dai, wa’adin shekara hudu ne aka tanadar wa Shugaban Kasa a zangon farko, inda yake da ikon sake neman wani zangon na shekara hudu a karo na biyu.

A matsayinmu na ’yan kasa masu ’yanci, mu sanya a zuciyarmu cewa, shin shekara hudun da ke tafe, yaya muke so su kasance? Muna son mu ga gyara a rayuwarmu da sana’armu, da aikinmu da kiwon lafiyarmu da sauransu? Tabbas muna son haka, babu wanda zai ce maka bai son ci gaba.

Tun da abin haka ne, to kasancewar muna rike da KATIN ZABE, shi ne lasisin ci gaban rayuwarmu ta shekara hudu masu zuwa. Idan muka yi amfani da shi muka zabi Shugaban da ya dace, babu shakka za mu ga abin da muka zaba a kwaryarmu. Idan kuwa muka yi sakaci, muka saryar da katin zabenmu ga wani shagirgirbau, mashiririci, haddasuna, to abin da za mu gani ke nan a shekara hudu masu zuwa – Shiririta.

Hausawa sun ce, mai kamar zuwa kan aika, kamar yadda suka ce da itace mai kama ake yin kota. Haka sun ce, ba a ba kura ajiyar nama. Duk me wadannan karin maganganu ke nufi a wannan lokaci?

Batun cewa mai kamar zuwa akan aika na nufin cewa, shugaban da za ka zaba a ranar 16-02-19, dan aike ne. Za ka aike shi ne ya wakilci rayuwarka gaba daya. Don haka sai ka kula da wanda ya fi cancanta ka aika domin ya kiyaye dukan rayuwarka, domin kuwa da itace mai kama ake yin kota. Kana bukatar itace mai kwari, mai siffa mai kyau ba karkatacce ba.

A lokacin da ka nufi mika ajiyar nama, kada ka sake ka mika wa kura, domin kuwa kura burungu daguyau ce, har da gashi ma ci take. Don haka kada mu biye wa dadin baki, kada mu biye wa alkawarin karya da karairayi. Mu waiga baya mu ga wane ne AMANA, da GASKIYA da ADALCI suke cikin rayuwarsa? Shi ne abin zabi!

Kafin zuwan wannan rana, a matsayinka na dan kasa mai kishi kuma mai son ci gabanta, ya kamata ka bambance tsakanin aya da tsakuwa. Ya kamata ka gane cewa wannan zabe, takara ce tsakanin karya da gaskiya, yaki ne tsakanin zalunci da adalci. Kai kuma, kana daga cikin dakarun da za su fafata a fagen daga, domin ’yanto kasarka, domin mika ta ga hannun Gaskiya da Adalci.

Kana rike da babban makami, wanda da shi za ka yi amfani a fagen daga a ranar 16-02-2019. Katin zabenka shi ne makaminka, kada ka sake ka bari azzalumai su kwace maka shi, kada ka sake azzalumai su raba ka da shi da kudi, ko nawa suka ba ka.

Ga ’yan siyasa kuwa, ku ma wannan fadakarwa ba za ta bar ku haka ba. Ya kai dan siyasa! Kowace jam’iyya kake, ya kamata ka sanya wa ranka tunani mai kyau, ka sanya wa ranka kudirin yin siyasa mai tsabta, wacce za ta taimake ka, ta taimaki al’ummarka, sannan kuma ta taimaki kasarka gaba daya.

Ya kai dan siyasa! Ka sani cewa kana da babbar damar da Allah Ya ba ka, wacce za ka iya kawo sauyi na kirki ga al’ummarka. Don haka ina jan hankalinka ka tabbatar ka yi tarayya da jam’iyyar kwarai, ka yi tarayya da ’yan siyasa na kwarai, domin ku gara siyasa ta kwarai domin cimma kudirori na kwarai.

Ya kai dan siyasa! Ka sani cewa duk abin da ka aikata a yau, shi ne tarihinka na gobe da jibi da har abada. An yi ’yan siyasa a jiya, sun taka rawar siyasa a jiya, a yau abin da suka shuka, shi ne yake bin su, yake bin ’ya’yansu da jikokinsu, na alheri ko akasinsa.

Ya kai dan siyasa! Da kake son jibintar al’amuran mutane, ina son ka shirya kanka, ka nazarci abin da al’ummar Najeriya ke bukata. Ka shirya yadda za ka hada kan al’umma na kowace shiyya.

Najeriya na da mabambantan al’ummomi, masu mabambantan al’adu da mabambantan addinai. Ya kai dan siyasa! Ta yaya za ka yi amfani da wadannan bambance-bambance wajen dinke al’umma wajen yi musu hidima domin ci gaban kasa?

Za mu ci gaba