Fadan kabilanci ya salwantar da rayuka a Habasha
Fadan kabilancin kasar Habasha ya salwantar da rayukan daruruwan mutane a fafatawar da aka yi tsakanin kabilun Oromo da Somali, lokacin da wsdannan manyan kabilun kasar ke takaddamar wane ne zai rike makiyayar kasa, da ke tsakaninsu. Fadan kabilancin ya barke tsakanin wadnanan manyan kabilu, har ta kai ga an kashe daruruwan mutane an tarwatsa […]

Fadan kabilancin kasar Habasha ya salwantar da rayukan daruruwan mutane a fafatawar da aka yi tsakanin kabilun Oromo da Somali, lokacin da wsdannan manyan kabilun kasar ke takaddamar wane ne zai rike makiyayar kasa, da ke tsakaninsu.
Fadan kabilancin ya barke tsakanin wadnanan manyan kabilu, har ta kai ga an kashe daruruwan mutane an tarwatsa dubbai daga gidajensu, kamar yadda gwmanati ta sanar.
Wadnanan kashe-kashe sun samo asali ne kan takaddamar mallakar makiyaya da kabilun Oromo da Somali da ke kudancin kasar suka dade suna yi, a cewar mai amgana da yawun gwamnati Negeri Lencho.
“Za mu iya cewa an halaka daruruwan ’yan kabilar Oromo, kuma akwai wadanda suka rasa rayukansu a bangaren Somali, ba mu dai san hakikanion adadinsu ba,” a cewar Negeri kamar yadda ya bayyana wa traron ’yan jarida.
An daidai fata fadan ne a kan iyakar jihohin kabilun, amma tuni aka kashe wutar rikicin, a cewar Negeri.
Tarayyar kasar Habasha dai kanta ya rabu a tsakanin yankunan Oromo da Somali, waddanda suka shafe tsawon shekaru suna takaddama kan wanda zai mallaki makiyayar da suke amfani da ita a kan iyakarsu.
A kuri’ar raba gardama da aka kada cikin shekarar 2004, duk da haka an ci gaba da karon-batta, inda aka rika zargin juna da amfani da sojojin kabilunsu.
A Afirilun bana, shugabannin yankunan sun rattaba hanu kan yarjejeniyar kwantar da rikici.
Negeri ya ce sojojin kabilar Somali sun kama jami’an gwmanati biyu daga yankin Oromia sun kashe su ranar 11 ga Satumbar bana, al’amarin da ya ruruta wutar rikicin tare da mummunar zanga-zanga a bangare Oromo.
An kafa rundunar kawo zaman lafiya ta kasa don shawo kan lamarin, tare da tarairayar wadanda aka tarwatsa daga garuruwansu, waddanda shugaban Oromo Lemma Meghersa a makon da ya wuce ya kimamnta adadinsu da cewa sun kai dubu 50. A halin yanzu dai ana ta kokarin sasantawa tsakanin shugabannin kabilun.