Fadan miji da mata

Wani magidanci ne ya samu matsala da matarsa, ta kai fagen ba su ko yin magana da juna. Sun xauki dogon lokaci a haka sai rannan buqata ta kama mijin, a ma’aikatarsu za a yi musu intabiyu domin qarin girma. An nemi su isa ofis da wuri, aka ce duk wanda bai je ofis da […]

Fadan miji da mata
Fadan miji da mata

Wani magidanci ne ya samu matsala da matarsa, ta kai fagen ba su ko yin magana da juna. Sun xauki dogon lokaci a haka sai rannan buqata ta kama mijin, a ma’aikatarsu za a yi musu intabiyu domin qarin girma. An nemi su isa ofis da wuri, aka ce duk wanda bai je ofis da qarfe shida ba, to ya faxi, ba za a qara masa girma ba. Saboda haka, mutumin nan yana son ya tashi da qarfe biyar na asuba, domin ya shirya, kuma ga shi yana son ya gaya wa matarsa ta taimaka ta tashe shi a lokacin. Maimakon ya nemi sasanci da matar tasa sai girman kai ya hana shi. Ya samu takarda ya rubuta cewa: “Don Allah ki tashe ni da qarfe biyar na asuba.” Lokacin da ya farka daga barci da safe, ya duba agogo sai ya ga har qarfe tara ta yi. Ya buga wani uban tsaki, ya tashi da fushi zai je ya ci zarafin matar tasa, sai ya ga wata takarda kusa da matashin kansa. Da ya xauka ya buxe, sai ya ga ashe matarsa ce ta rubuta ta da qarfe biyar na asuba. Abin da ta rubuta shi ne: “Ka tashi, yanzu qarfe biyar daidai.”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08098157899.