FADAR FDQ: Sakonnin fadakarwa dangane da soyayya

Martani: FDQ, dangane da mutumin nan da ya ce an yaudare shi a Malumfashi, idan an bi ta barawo sai kuma a bi ta mabi sawu. Abin tambaya shi ne, shi bai taba yaudarar wata ba? Sannan tun da ya je Kano, ya kuma waiwayarta ko kuwa ita wane dalili ta ba da? Domin sharrin […]

FADAR FDQ: Sakonnin fadakarwa dangane da soyayya

Martani:

FDQ, dangane da mutumin nan da ya ce an yaudare shi a Malumfashi, idan an bi ta barawo sai kuma a bi ta mabi sawu. Abin tambaya shi ne, shi bai taba yaudarar wata ba? Sannan tun da ya je Kano, ya kuma waiwayarta ko kuwa ita wane dalili ta ba da? Domin sharrin ’yan uwana maza yawa ne ke da shi. Duk abin da ka yi wa wani, za a yi maka.

Daga Muhammad Hassan Danbaza, 07068040761.

 

Jinjina ga mata:

FDQ, dole, mu yaba wa mata, mu yi masu jinjinar girma, mu yi kirari mu ce: ‘Mata na inna dangin wane, in ba ku ba gida, in kun yawa gida sai shukura!’ FDQ kalubalenka yau shi ne, ka ci gaba da nuna wa mata matasa cewa su ji tsoron Allah. Su yi zaman auren amana. Su yi hakuri da biyayya ga mazansu na aure. Su zauna lafiya da kishiya, su yi wa ’ya’yansu tarbiya. Su nemi ilimi, su koyi sana’a. Su yi wa Allah godiya da ya ba mu ’ya’ya mata masu yawa, don haka mata ku ba mazanku goyon bayan kara aure. Mata darajarku na da yawa, ku ne fa tubalin samar da al’umma. Allah saka maku da alheri.

Daga Amiru Bakori, 07068147933.

 

Ku ba ni shawara:

FDQ jagoran masoya, da fatan kana lafiya. Don Allah ina so a ba ni shawara a kan tsohuwar budurwata, wacce shekara goma muna tare. Har na kai kudi gidansu, sai wata rana ta zo tana gaya mani cewa wai iyayenta sun ce za su aura ta ga dan wan babanta. Na ji ba dadi amma na bar wa Allah komai. Yau shekara biyar ke nan, har na manta da komai sai kawai aka zo gidana aka ce ana sallama da ni. Da na fito sai na ga cewa ita ce. Sai take gaya mani cewa wai mijinta ya sake ta saki uku. Ban ji dadi ba, ta ce ita tana nan a kan bakanta; ni kuma na samu madadinta. Don Allah a ba ni shawara, yaya zan yi?

Daga Baban Abbas Kano, 08033996529.

***

Malam Baban Abbas, na farko ka ce ka riga ka samu makwafinta, ba shi ke nan ba? Amma kuma idan har yanzu kana sonta kuma kana son kara aure, to ina shawartarka da ka yi bincike, yaya aka yi har mijinta ya yi mata saki uku? Amsar da ka samo, ita za ta ba ka kwarin gwiwar aurenta ko akasin haka. – FDQ.

 

Ina son shafin nan:

Fatan alheri ga FDQ da kuma daukacin almajiran makarantar Dausayin Qauna. A gaskiya wannan fili ya shiga raina, kodayaushe na sayi Aminiya, wannan shafin shi ne shafin farko da nake fara karantawa. Ina fatan FDQ zai ci gaba da ninkaya da mu a cikinsa. Allah Ya kara wa Aminiya daukaka.

Daga Shamsu Xan’iya Suleja, 08036160154.

 

Gare mu mata da maza:

Assalamu alaikum, fatan alheri a gare ku masoya wannan fili. A kowane lokaci muna jin yadda mata ke aikata abubuwa da dama, to kada wani ya karaya ya kasa aure. Ba za ka iya cewa dukkan mata halinsu daya ne ba. Mu dai fatanmu Allah Ya ba mu mazaje nagari, mazan ma Allah Ya ba su mata nagari, amin.

Daga Farida Bamalli, 07038620271.

Nasiha ga masoya

Fatan alheri gare ka FDQ, ina so in tunatar da masoya wani al’amari mai girman gaske. Yaudara, karya, muna yawan ambatarsu a wannan shafi namu mai albarka amma muna manta matsayin hukuncinsu a addininmu!

Akwai hadisi ingantacce Manzon Allah (s.a.w) yana cewa “alamun munafiki guda uku ne, ko da ya yi Sallah, ya yi azumi kuma ya yi ikirarin shi Musulmi ne. Idan zai yi magana ya yi karya, idan an yi alkawari ya saba, idan an amince da shi ya yi yaudara.” Allah Ya nisanta mu daga karya da yaudara.

Daga Abdul’azeez Abu Zayd Funtuwa, 08168969329.