Fadar Sarkin Dass ta raba zakkar buhu 240
Fadar Sarkin Dass da ke Jihar Bauchi ta raba zakkar kayan abinci da suka kunshi masara da gero da dawa da shinkafa da waken soya buhu 240 da kuma shanu biyu ga mabukatan yankin. Kwamishinan Zakka a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi Alhaji Tata Alkaleri ne ya jagoranci raba zakkar a garin Dass, inda ya […]
Fadar Sarkin Dass da ke Jihar Bauchi ta raba zakkar kayan abinci da suka kunshi masara da gero da dawa da shinkafa da waken soya buhu 240 da kuma shanu biyu ga mabukatan yankin. Kwamishinan Zakka a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi Alhaji Tata Alkaleri ne ya jagoranci raba zakkar a garin Dass, inda ya yaba wa sarakunan da suka bayar da zakkar tare da jan hankalin sauran mutane su yi koyi da su wajen fitar da hakkin Allah a cikin dukiyar da Ya hore musu in ta kai nisabi. Ya ce hukumar ta himmatu wajen shiga sassan jihar domin raba zakkar kudi da dabbobi da kayan abinci don a kara karfin guiwa ga mutane saboda su sauke hakkin Allah da Ya rataya a wuyansu.
Cikin wadanda suka bayar da zakkar akwai Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman wanda ya bayar da buhu 23 sai Bunun Dass buhu 10, sai dankaden Dass buhu 185, sai dan-Rimin Dass buhu 10 sai Sa’in Dass buhu daya sai Alhaji Ibrahim dankade buhu 11 yayin da Alhaji Bayu ya bayar da shanu biyu. Ustaz Gidado Umar, wakilia Hukumar Shari’a ya gode wa mutanen da suka bayar da zakkar tare da jan hankalin Musulmi su sauke nauyin da Allah ya dora musu don su tsarkake dukiyarsu ta zamo mai albarka. Ya ce bayar da hakkin Allah na taimakon marasa karfi a kowane lokaci, kuma zakka aiki ne da bai dace sai an bi kan mutane ba, kafin su bayar. Ya ja hankalin Musulmi su kasance masu bin dokokin Allah domin samun makoma tagari ranar gobe kiyama.