Fadar Shugaban Kasa ta ƙaryata tayin N105,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Sam Ministan Kuɗi bai ba da shawarar ƙayyade Naira 105,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.
Fadar Shugaban Kasa ta ƙaryata rahotan da ake yaɗawa cewa Ministan Kuɗi, Wale Edun ya miƙa tayin Naira 105,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.
A bayan nan dai ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aikin da shiga bayan kulla yarjejeniyar sulhu a tsakaninta da Gwamnatin Tarayya.
Sai dai bayan ganawar da ya yi da tawagar sulhun da Gwamnatin Tarayya ta wakilta, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Ministan Kuɗi wa’adin sa’o’i 48 domin cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.
Dangane da hakan ne Ministan Kuɗin da tawagarsa suka ba da shawarar ƙayyade Naira 105,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce babu ƙamshin gaskiya kan wannan batu.
Onanuga ya ce “ba gaskiya ba ne cewa Ministan Kuɗi ya ba da shawarar ƙayyade Naira 105,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
“Wannan ba gaskiya ba ne sabanin rahotannin da ake yaɗawa,” a cewar saƙon da Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.