Fadar Shugaban Kasa ta koka kan karancin kudin tallafi
Fadar Shugaban Kasa ta ce kasar tana fuskantar karancin kudi da fasahar zamani don kai agajin gaggawa ga dimbin mutanen da bala’o’i suka aukawa a kasar. Fadar ta bayyana cewaduk da haka gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta yi bakin kokarinta ta kai agajin gaggawa ga wadanda bala’i ya aukawa a kasar. Babban Mai Taimakwa Shugaban […]

Fadar Shugaban Kasa ta ce kasar tana fuskantar karancin kudi da fasahar zamani don kai agajin gaggawa ga dimbin mutanen da bala’o’i suka aukawa a kasar.
Fadar ta bayyana cewaduk da haka gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta yi bakin kokarinta ta kai agajin gaggawa ga wadanda bala’i ya aukawa a kasar.
Babban Mai Taimakwa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Yada Labari da Wayar da Kan jama’a, Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana haka a shirin Hannu da Yawa na gidan Rediyon Kaduna wanda aka gabatar a karshen mako.