Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan kamuwar Sarki Abba da coronavirus

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da labarin da ta misalta a matsayin karya wanda wani kamfanin jarida na zamani ya wallafa da cewa Hadimi na Musamman kan Harkokin Cikin Gida ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kamu da cutar coronavirus. A jawabin tabbatar da wannan lamari a matsayin kanzon kurege da ya fitar a ranar […]

Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan kamuwar Sarki Abba da coronavirus

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da labarin da ta misalta a matsayin karya wanda wani kamfanin jarida na zamani ya wallafa da cewa Hadimi na Musamman kan Harkokin Cikin Gida ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kamu da cutar coronavirus.

A jawabin tabbatar da wannan lamari a matsayin kanzon kurege da ya fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu ya ce Sarki Abba bai kamu da cutar ba.

Mallam Garba ya ce dukkan ma’aikatan da ke zagaye da kuma kusantar Shugaba Buhari, ana yi masu gwajin cutar akai-akai domin tabbatar da lafiyar Shugaban Kasa.

Ya ce Sarki Abba yana cikin sahun ma’aikatan da sakamakon gwajinsu bai taba nuna suna dauke da kwayoyin cutar ba.

“Saboda haka Fadar Shugaban Kasa na son bai wa ’yan Najeriya shawara da su yi watsi da dillancin yada labaran karya a tsakanin al’umma.

“Muna martani kan shaci-fadi da labaran bogi da wata jaridar zamani ke yadawa da cewa hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Sarki Abba ya kamu da cutar COVID-19.

“Wannan rahoto baya dauke da kamshin gaskiya kuma babu abin da mawallafansa suka nufata face batar da al’umma.

“Sakamakon bin umurnin likitoci da masana kimiya da kuma sa ido da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari ke yi, ana yi wa dukkannin ma’aikata da masu kusantar Shugaba Buhari gwajin cutar akai-akai.

“Hadimin Shugaban Kasar kan harkokin cikin gidan, Sarki Abba, bai taba kamuwa da cutar ba.

“Saboda haka kada ku bari wata kafar watsa labarai ta jefa ku cikin rudu ko yaudara musamman a yayin da suka kware wajen cin kasuwarsu da wallafar rahotanni na karya”, inji sanarwar.