Fadar shugaban kasa ta mayar wa Sule Lamido martani
Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido kan sukar da ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari. A sanarwar da ya fitar, Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kai, Garba Shehu ya ce bai kamata a ce Lamido na neman shugaban kasa […]

Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido kan sukar da ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari.
A sanarwar da ya fitar, Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kai, Garba Shehu ya ce bai kamata a ce Lamido na neman shugaban kasa ba saboda shari’ar da yake fuskanta a kotu.
Shehu ya bayyana hirarrakin da Lamido ya yi da manema labarai na sukar Buhari kan yakin da yake yi da cin hanci a matsayin wata alama da ke nuna irin yadda ’yan adawa suke a Najeriya.