Hajara Sanda: Fadi-tashin zama farfesa mace a fannin jarida

Hajara Sanda ita ce mace ta farko da ta zama farfesa a fannin koyar da aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano

Hajara Sanda: Fadi-tashin zama farfesa mace a fannin jarida

Farfesa Hajara Sanda

Hajara Umar Sanda it ace mace ta farko da ta kai matsayin farfesa a sashen koyar da aikin jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano.

A ’yan kwanakin nan wata kungiya mai suna MassMediaNG ta karrama ta a matsayin daya daga cikin mata farfesoshi goma a fannin koyar da aikin jarida a Najeriya.

A cikin wannan tattaunawar, ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha har ta kai ga matsayin, musamman kasancewarta Bahaushiya daya tilo mai sanya hijabi a jerin wadanda aka karrama din.

Ya ya ki ka ji da karramawar da aka yi miki a matsayin daya daga cikin mata farfesoshi a bangaren koyar da aikin jarida a Najeriya?

A ranar 26 ga watan Agusta na samu wani sako ta dandalin sada zumunta na WhatsApp a wayata, bayan na bude shi sai na ga wani bidiyo da ke dauke da mata farfesoshi guda goma da ke kan gaba a fannin koyar da aikin jarida a Najeriya.

Abin mamaki ne matuka, saboda ban ma san su waye suka shirya shi ba.

Na damu matuka da yadda aka ambaci sunana a ciki saboda ban kai ga zama cikakkiyar farfesa ba tukunna.

Sai na yi kokarin samun lambar wayar wanda ya kirkiri shafin na MassMediaNG wanda shi ma yana dab da zama farfesa a fannin, inda ya tabbatar min da cewa suna karrama matan da suka yi fice ba lallai farfesoshi ba; a’a har ma wadanda suke dab da zama.

Ya ce min sukan duba abin da ya bambanta su [matan] da sauran da zai sa su zama zakarun gwajin dafi tsakanin takawarorinsu tare da karrama su da kyauta yayin bikin da za su gudanar na bana mai taken ‘Ranar Samar da Daidaiton Mata ta 2020’.

Sun kuma hada da wasu farfesoshi guda biyu masu mukamin emeritus.

Ya kuma shaida min cewa baya ga wadannan, sun kuma zabe ni ne kasancewar ni ce mace ta farko da ta kai wannan matsayin a sashenmu na Jami’ar Bayero inda suka kalli hakan a matsayin wani abu da zai kara karfafa cigaban ilimin ’ya’ya mata a Arewacin Najeriya.

Sun kuma ce na bayar da muhimmiyar gudunmawa a bangaren aikin jarida.

Mu uku ne mata aka zaba daga Arewacin Najeriya: Daya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, dayar daga Jami’ar Jos sai kuma ni.

Gaskiya na dauki hakan a matsayin wata muhimmiyar girmamawa.

Sun ce bangaren da na fi mayar da hankali a wajen bincikena (Batutuwan da Suka Shafi Lafiyar Mata a Arewacin Najeriya) ne ya fi burge su.

Kazalika, sun ce ina daya daga cikin mata kalilan a Arewacin Najeriya masu koyar da aikin jarida da suka sami tallafin karo karatu zuwa Fulbright a kasar Amurka.

Mene ne sirrin jajircewarki har kika kai ga wannan matsayin?

Akwai wani salon magana da ke cewa duk abin da namiji zai yi, mace ma za ta iya yi ko ma fiye da haka.

Na tsinci kaina a cikin irin wani wuri da maza suka yi wa kaka-gida yayin da ake da mata ’yan kalilan, hakan ya karfafa min gwiwa wajen kara zage damtse.

Na kuma kara samun kwarin gwiwa lokacin da na sami tallafin karo karatu na Fulbright a kasar Amurka domin yin digirin-digirgir dina.

Wani kuma abin da ya kara karfafa min gwiwa shi ne ina son zama abar koyi ga ’ya’ya mata a Arewacin Najeriya.

Shin akwai wani kalubale da kika ci karo da shi a wannan fadi-tashin?  

Farkon dauka ta aiki a matsayin malamar jami’a kalubale na farko da na fara fuskanta shi ne na yadda nake shiga.

Mutane da dama sun rika yi min kallon raini saboda yadda nake saka hijabi, inda wasunsu ma ke tunanin ba zan iya tabuka wani abin ku-zo-ku-gani ba.

Wannan babban kalubale ne a wuri na, wanda shi kansa ya sa dole in tashi tsaye wajen ganin na ba mara da kunya.

Bugu da kari, tafiyata zuwa Amurka ita ma ta zo min da kalubale kasancewar dole na tsallake na bar iyalaina.

Amma Alhamdulillahi sakamakon hadin kan da na samu daga mijina da mahaifiyata komai ya zo min da sauki. Ina matukar godiya gare su.

Wani kalubalen da kuma na sake fuskanta shi ne tafiyar hawainiya a karin matsayin da ya kamata a yi min a aiki bayan kammala karatun digirina na biyu a kan wani dalilin da bai taka kara ba ballantana ya karya.

Amma daga bisani kuma aka yi wa wani abokin aikina namiji da yake da makamanciyar matsala irin tawa a wani sashen. Ba zan taba mantawa da wannan ba.

Kazalika a shekara ta 2012 bayan dawowata daga Amurka bayan kammala digirina na uku, na dawo da kammalallen rubutuna wanda na yi a karkashin kulawar malamin da ya duba min aikin.

Amma bayan na dawo Najeriya sai aka yi watsi da ni da gangan na kusan shekaru biyu ba tare da an kira ni na zo na kare aikina ba.

Dalilin ke nan da ya sa na kammala a shekarar 2014 a maimakon 2012 ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

A matsayina na mace, maimakon a karfafa min gwiwa duk da cewa na tafi na bar dukkan iyalaina na samu na kammala a kan lokaci, sai aka yi watsi da ni.

Shin akwai lokacin da kika taba jin kin kusa sarewa?

Babu. Mun shafe shakara biyar muna kokarin kammala karatun digiri na biyu, akwai daya daga cikin ’yan ajinmu ma da ya tafi kasar Ingila daga bisani kuma ya samu ya kammala karatunsa a watanni tara.

Amma ni ban taba sarewa ba. Ni na yi amanna da ci gaba da fafutuka har na kai ga cimma nasara.

Ta yaya kika kai ga cin nasara kan wadannan kalubalen?

Na yarda da jajircewa. Akwai dadi da rashin dadi a rayuwa, amma hakuri da jajircewa su ne mabudin nasara.

Mijina da mahaifiyata kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen ba ni gudunmuwa.

Shin ya kika ji kan tafiya kasar waje kika bar iyalanki saboda neman ilimi? 

Kafin na kai ga samun tallafin karo karatun na Fulbright, mutane da yawa sun shaida min cewa ko na samu ba zan iya tafiya ba.

Lokacin da aka gayyace ni jarrabawar tantancewa wasu ma sai da suka nemi sare min gwiwa wai kada na je, kuma ko da na samu ma mijina ba zai bar ni na tafi ba.

Amma cikin ikon Allah mijina kasancewarsa lauya kuma mai fafutukar ilimin mata ya ba mara da kunya, ya tsaya tsayin daka wajen tallafa min har na kammala karatun.

Ko lokacin da ina can Amurkan sai da ya kawo min ziyara lokacin da na kusa kammalawa muka dawo tare.

Na kuma sami tallafi daga hukumar jami’a da kuma abokan aiki na da ke sama da ni a jami’ar.

Haka kuma ina yaba wa Sashen Al’adu na Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya saboda gagarumar damar da suka ba ni. Ina matukar godiya gare su gaba daya.

Me kike ganin ya kamata a yi don bunkasa ilimin ’ya’ya mata musamman a yankin da kika fito na Arewacin Najeriya?

Akwai wani salon magana da ke cewa in ka ilmantar da da namiji ka ilmantar da mutum daya ne, amma in ka ilmantar da ’ya mace, tamkar ka ilmantar da alumma ce baki daya.

Mun san cewa ilimin ’ya mace yana da muhimmanci musamman a Arewacin Najeriya inda lamarin tabarbarewar ya fi kamari.

Yawanci akan fake da talauci da jahilci wajen dora musu talla da yi musu auren wuri.

Dole gwamnati ta shiga lamarin ta hanyar bayar da ilimi kyauta a kowane mataki gare su a Arewa.

 Na shiga kungiyoyi masu zaman kansu da dama da ke fafutukar karfafa gwiwar mata, ciki har da kungiyar tsofaffin daliban makarantata ta Shekara (SHOGA) inda muka yi abubuwa da dama wajen inganta ta har ta kai ga mun gina mata dakin shan magani.

Bugu da kari, kungiyarmu ta tsofaffin daliban Jami’ar Bayero aji na 1992 ta yi ayyuka da dama na cigaban al’umma.

Ina kuma cikin wata gidauniya da take mayar da hankali wajen bayar da tallafin karo karatu ga dalibai musamman mata da kuma masu bukata ta musamman.

Shin kina kallon nasarar da kika samu a rayuwa a matsayin abin da zai taimaka wajen kawo karshen kallon da ake wa mata a Arewa?

E hakika, na tabbata, wannan kuma somin tabi ne ma.

Na yi amanna cewar sinadaran cin nasara su ne aiki tukuru, gaskiya, hakuri, tsayawa kan gaskiya da rikon amana da kuma uwa uba tsoron Allah.

Ina shawartar ’yan uwana mata da su kara kokari domin ganin su ma sun kawo karshen irin kallon da ake yi wa mata kuma a ji sunansu a duniya.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara