Faduwar Abdeláziz Bouteflika

Shugaban kasar Aljeriya Abdeláziz Bouteflika wanda ya dade kan karagar mulki kuma  mai fuskantar kalubale ya yi murabus a makon jiya bayan shafe makonni ana zanga-zangar  nuna kyamar mulkinsa. Bouteflika dai ya shafe shekara 20 a kan karagar mulki. Shugaban na kama-kayar mai shekara 82, ya samu cikas ne bayan da aka ayyana cewa ba […]

Faduwar Abdeláziz Bouteflika

Shugaban kasar Aljeriya Abdeláziz Bouteflika wanda ya dade kan karagar mulki kuma  mai fuskantar kalubale ya yi murabus a makon jiya bayan shafe makonni ana zanga-zangar  nuna kyamar mulkinsa. Bouteflika dai ya shafe shekara 20 a kan karagar mulki. Shugaban na kama-kayar mai shekara 82, ya samu cikas ne bayan da aka ayyana cewa ba ya da cikakkiyar lafiyar da zai iya gudanar da ayyukansa na mulki. Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin Shugaban Rundunar Sojin Aljeriya, Ahmed Gaid Salah,  wanda ya ce Bouteflika wanda ya samu matsalar bugun zuciya kimanin shekara shida da suka gabata tun daga wancan lokaci ya daina bayyana a bainar jama’a sosai sannan ba ya iya gabatar da ayyukansa na Shugaban Kasa, tare da zargin cewa wadansu na hannun damarsa ne da kuma wadansu jiga-jigan ’yan kasuwa suke amfani da shi don cimma burinsu. Majalisar Tsarin Mulki ta Kasar ta amince da murabus din nasa a ranar Larabar makon jiya, wanda hakan a hukumance ya kawo karshen mulkin mutumin da ya yi kaka-gida a kan sha’anin siyasar kasar tare da barinta cikin wani hali na rashin tabbas.

Zanza-zangar da aka rika yi ta jawo kiraye-kirayen a kawo  sauye-sauye kan  yadda ake gudanar da siyasar kasar wacce sojoji suke taka gagarumar rawa a ciki. Sakamakon murabus din Bouteflika, Shugaban Majalisar Dattawa, Abdulkader Bensalah yanzu shi ne Shugaban Rikon kasar. A ranar  Talata 9 ga Afirilu ne aka sa ran majalisar za ta zauna don samar da Shugaban Kasa na rikon-kwarya wanda zai shugabanci tsarin mayar da mulkin dimokuradiyya bayan shekara 60 da tsofaffin sojin suka jagoranci yakin kwatar ’yanci daga kasar Faransa a shekarar 1954 zuwa 1962.

A karkashin kundin tsarin mulkin kasar Aljeriya dai, majalisar tana bukatar ta gabatar da kudirin tabbacin gurbin kujerar Shugaban Kasa tukuna, daga bisani sai ta zabi Shugaban Rikon Kwarya wanda zai ci gaba da gudanar da mulki da tsare-tsare har na wata uku sannan zabe ya biyo baya. To amma shi kansa Bensalah wanda shi ne Shugaban Majalisar da zai zama Shugaban  Riko yana fuskantar matsi daga masu zanga-zanga a kan sai ya yi murabus tare da Firayi Minista Nouredine Bedoui  da kuma Shugaban Majalisar Tsarin Mulki Tayeb Belaiz wadanda duk ake yi musu kallon na kusa da Bouteflika. Masu zanga-zangar suna son a yi sabon lale ne a siyasar kasar amma kuma wadannan uku duk suna daga cikin karnukan farautar da suka mara wa Bouteflika baya har ya shafe shekara 20 a kan karagar mulki.

Duk da yake masu zanga-zangar sun  yi nasarar tsige Shugaba Bouteflika daga kan mulki ba tare da rasa koda ran mutum daya ba ko yin amfani da bakin bindiga, ana ganin yanzu ne fafutikar kawo canjin ta fara. Masu zanga-zangar dai sun yi cikkakken tsari kuma sun yi wa zanga-zangar lakabi da taken “Kawar da tsari”  ko  “Yin waje da tsari!” Saboda haka duk wani da yake da alaka da gwamnatin Bouteflika a wajen masu zanga-zangar abin tuhuma ne. Abin da kawai suke bukata shi ne garambawul da sababbin shugabanni da sabon zabe da sabuwar gwamnati. Amma babbar tambayar ita ce, shin zai yiwu jami’an soji su bar hakar masu zanga-zangar ta cimma ruwa ta kawo gyara ga “tsarin.” Shi kansa Janar Salah, wanda a halin yanzu yake ikirarin goyon bayan masu zanga-zangar daya ne daga cikin wadanda suka gudanar da tsohon tsarin na kama-karya.

Sojoji ne suke yin kane-kane a duk wani abu da ya shafi siyasar kasar Aljeriya tun bayan da kasar ta samu’yancin kanta. A wannan lokaci ma, sojin ne dai suka hura wa Bouteflika wuta har ya sauka. Domin idan babu goyon bayansu zanga-zangar ba ta isa ta kawar da tsohon Shugaban daga kan kujerarsa ba. Ta bangaren sojin kuma babu tabbacin cewa suna son su mika ragamar mulkin kasar kacokan ga hannun farar hula. Wannan yanayi ne mai rikitarwa, amma dai tunda yake sun fafata shekaru suna Yakin Basasa sannan suka sake shafe shekara ashirin a cikin mulkin kama-karya, jama’ar kasar Aljeriya suna bukatar a yi wa kasarsu kwaskwarima.

Masu zanga-zangar sun gabatar da bukatar kubutar da kasar daga wadanda suka ce sun wofintar da tattalin arzikin kasar. Sannan  tabbatar da tsarin siyasar kasar sannan  duk wadansu masu wuka da nama a gudanarwar kasar ciki har da sojoji da manyan kusoshin kasar su bayar da gudunmawarsu don jaddada zaman lafiya.

Shugabancin gina gwamnatin hadakar ta kasa wacce za ta gudanar da tsarin mayar da mulki ga farar hula bayan murabus din Boutflika koda a ce yana a hannun karnukan farauta ne wajibi ne ya tabbatar da gudanar da zabe da  mika mulki ga hannun farar hula cikin kwanciyar hankali da lumana.

Daga karshe, al’ummar kasar Aljeriya musamman ma matasa sun tabbatar da hadin kansu da kuma nuna taka-tsantsan wajen abin da ya shafi dambarwa da kalubalen da kasarsu ke fuskanta. Kuma sun nema wa kansu mutunci da kansu, ba tare da taimakon wata kasa ba. Wannan abin misali ne a siyasance wanda kuma zan fito da sababbin shugabannin kasar na nan gaba, wadanda za su cika sharuddan da jama’ar kasar ke bukata.