Faduwar darajar Naira ta jawo wa dangote asarar biliyoyin Naira

Mujallar Forbes da ke Amurka da ta bayyana Alhaji Aliko dangote a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka ta ce ya yi asarar Naira biliyan 14 da miliyan 860 a cikin kasa da mako uku a sakamakon hauhawar farashin Dala da kuma faduwar farashin danyen man fetur.Idan ba a manta ba Gwamnan Babban […]

Faduwar darajar Naira ta jawo wa dangote asarar biliyoyin Naira
Faduwar darajar Naira ta jawo wa dangote asarar biliyoyin Naira

Mujallar Forbes da ke Amurka da ta bayyana Alhaji Aliko dangote a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka ta ce ya yi asarar Naira biliyan 14 da miliyan 860 a cikin kasa da mako uku a sakamakon hauhawar farashin Dala da kuma faduwar farashin danyen man fetur.
Idan ba a manta ba Gwamnan Babban Bankin Najeriya  (CBN), Godwin Emefiele ya sanar da faduwar darajar Naira, inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon faduwar farashin man fetur da kuma tashin darajar Dala, inda Dala daya take daidai da Naira 187 maimakon Naira 164 a farkon makon watan Nuwamba. Hakan ya sanya tattalin arzikin Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 40 (Naira biliyan 880).
Dalilin hakan, inji Mujallar Forbes, ta sanya dangote ya yi asarar Dala biliyan 7.8 (Naira biliyan 14 da dubu 860). Mujallar ta ce a farkon makon watan Nuwamba dangote ya mallaki Dala biliyan 25 (Naira biliyan 34 da dubu 750), inda a ranar Talatar da ta gabata ya yi asarar Dala biliyan 7.8, inda arzikinsa ya koma Dala biliyan 17.2
Mai sharhi a kan tattalin arziki kuma mawallafin kafar sadarwa ta Nairametrics Ugodre Obi-Chukwu ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar nan ya shiga cikin mawuyacin hali ne sakamakon tashin darajar Dala da kuma faduwar farashin man fetur .
Sauran  ’yan Najeriya da wannan asarar ta shafa akwai  Tony Elumelu, wanda shi ne shugaban Kamfanin Heirs Holdings. A farkon makon watan Nuwamba Elumelu yana da Dala biliyan 1.4, amma a yanzu ya koma Dala miliyan 700, wanda hakan ya nuna ya yi asarar Dala miliyan 400.