Faduwar darajar Naira ta koma da dangote baya a jerin attajiran duniya
Faduwar darajar Naira ta sanya attajiri Alhaji Aliko dangote komawa baya a jerin attajiran duniya daga na 23 zuwa na 67, kamar yadda Mujallar Forbes da ke Amurka wacce ke fitar jerin sunayen attajiran duniya ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata. Mujallar ta ruwaito a watan Fabrairu, 2014 dangote ya mallaki Dala biliyan […]
Faduwar darajar Naira ta sanya attajiri Alhaji Aliko dangote komawa baya a jerin attajiran duniya daga na 23 zuwa na 67, kamar yadda Mujallar Forbes da ke Amurka wacce ke fitar jerin sunayen attajiran duniya ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata.
Mujallar ta ruwaito a watan Fabrairu, 2014 dangote ya mallaki Dala biliyan 25, amma sakamakon faduwar darajar Naira da kuma raguwar yadda ake bukatar siminti a ranar Litinin da ta gabata attajirin ya mallaki Dala biliyan 17 da dubu 700.
Mujallar ta bayyana har yanzu dangote shi ne a matsayina na daya a Afirka.
Sauran wadanda suka shiga jerin attajiran duniya daga Najeriya akwai Shugaban Kamfanin Sadarwa na Glo kuma Shugaban Kamfanin Mai na Conoil, Mista Mike Adenuga wanda yake matsayi na 393, inda ya mallaki Dala biliyan 4.2, wanda ya nuna shi ne attajiri mai matsayi na biyu a Najeriya.
Misis Folorunsho Alakija, mace baka attajira ta daya a duniya ita ce ta 949 a jerin sunayen attajiran duniya, inda ta mallaki Dala biliyan 1.9.
Shugaban Kamfanin Mai na Forte Oil, Mista Femi Otedola shi ne attajiri na hudu a Najeriya, inda yake da matsayi na 1741 a duniya, inda ya mallaki Dala biliyan 1.
Shi ma Shugaban Kamfanin BUA Abdulsamad Rabiu ya mallaki Dala biliyan 1, inda yake matsayi daidai da na Otedola.
A kowace shekara mujallar tana fitar jerin sunayen attajiran duniya, inda a wannan karon attajiri dan a Amurka Bill Gates wanda ya mallaki kamfanin Microsoft ya zama attajirin duniya a karo na 16 cikin shekara 21.
Attajirin nan dan kasar Medico Carlos Slim shi ne ya zo matsayin na biyu.
An kiyasta dukiyar Mista Gates ta havaka daga Dala biliyan 3 a watan Fabrairu, 2014 zuwa Dala biliyan 79 a ranar Litinin.
Warren Buffett dan kasar Amurka shi ne a matsayi na uku inda ya mallaki Dala biliyan 72.7 .