Faduwar jarrabawar WAEC laifin wane ne?

A kwanakin baya Darakta mai kula da ofishin kasar nan na Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma da ake ma lakabi da WAEC Mista Charles Eguridu, ya bayyana sakamakon jarrabawar da daliban kasar nan da suka kammala ilminsu na babbar Sakandare tsakanin watannin Mayu da Yunin bana suka kuma zana jarrabawar Hukumar, jarrabar da […]

Faduwar jarrabawar WAEC laifin wane ne?
Faduwar jarrabawar WAEC laifin wane ne?

A kwanakin baya Darakta mai kula da ofishin kasar nan na Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma da ake ma lakabi da WAEC Mista Charles Eguridu, ya bayyana sakamakon jarrabawar da daliban kasar nan da suka kammala ilminsu na babbar Sakandare tsakanin watannin Mayu da Yunin bana suka kuma zana jarrabawar Hukumar, jarrabar da ya ce sakamakonta bai kai na bara armashi ba.
Bisa ga alkalumman da Daraktan ya bayar, daga cikin dalibai sama da miliyan 1.6, da suka zana jarrabawar, dalibai 529,425, suka samu nasarar cin darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi, wadanda kenan su suka cancanci shiga Jami`o`i da sauran manyan makarantun kasar nan ko na kasashen waje kai tsaye ba tare da wata hiyana ko tangarda ba. Wato dai sauran dalibai sama da miliyan 1, ba za su samu shiga irin wadancan manyan makarantu ba kai tsaye, har sai sun sake zana wata jarrabawar da aniyar su iya cikasa gibin da suke da shi.
Sakamakon na bana, ya kasance koma baya akan yawan daliban da suka yi nasara a irin wannan jarrabawa a bara da bara waccan. Alal misali, kashi 38, cikin 100, na daliban da suka zana jarrabar a shekarar 2012, su suka samu nasara, ya yin da kashi 36 cikin 100, na wadanda suka zana jarrabawar a shekarar 2013, su suka yi nasara, wato su suka ci darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi, kamar yadda ake bukata. Koma bayan sakamakon banan shi yake nuni da cewa tamfar ana neman a koma ’yar gidan jiya, wato sakamakon shekarar 2010 da dalibai kashi 23, kadai suka yi nasarar aje a karar ko na shekarar 2004, da kashi 18 cikin 100, kadai suka yi nasara.
Idan da za ka bincika kusan dukkan sakamakon da ake samu din duk shekara za ka taras mafi yawan masu cin jarrabawar daga makarantu masu zaman kansu suke, ko gwari-gwari, mu ce na kudi, makarantun da suka yi kaurin suna a yau akan ba dalibansu satar amsar jarrabawa koma su rubuta musu, al`amarin da ya kai fagen yanzu har wasu makarantu ake da su da ake yi wa lakabi da “Makarantun banmamaki,” da ake kira a Turancin Ingilishi “Miracle Schools” da Turanci. A irin wannan makarantu masu su kan ba iyayen yara da idanuwansu suka rufe akan lallai sai `ya`yansu sun ci jarrabawa ko ta halin kaka tabbacin cewa, `ya`yan nasu za su ci jarrabawa akan darussan da suke so, ta yadda za su samu shiga manyan makarantu kai tsaye, ba tare da la`akari da kokari ko rashin kokarin `ya`yansu ba, su dai kawai su bada kudi don su samu biyan bukata.
Daga irin halin da harkokin ilmi suke ciki a kasar nan ka iya cewa tabarbArewar fanni yanzu aka fara, muddin Mahukunta (shugabannin siyasa) da Sarakuna da masu hannu da shuni da Iyaye da Malamai, ba su tashi tsaye ba suka kama ma wannan fanni mai matukar muhimmancin gaske kan ci gaban rayuwar kasa da al`ummar ta dama na duniya baki daya, don ai sai da ilmi ake kome tun tuni ba tun yau  ba, haka kuma za a ci gaba da yi har duniya ta tashi.
Ina ga lokaci ya yi da mahukunta musamman na jihohin Arewa, a Arewar ma, a Arewacin Arewa inda nan ake fama da koma bayan tabarbarewar ilmi tun ana ce wa Bature Zaki (don a kididdigar yaran da suka isa shiga makarantun Firamae da Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar dinkin Duniya wato UNICEF ya gudanar, ta tabbatar da cewa akwai yara sama da miliyan 10, da ba su zuwa makarantun Firamare kuma kashi kusan 50 cikin 100, ko mu ce rabinsu, suna shiyyar Arewa maso Yamma, wato shiyyar da ta kunshi jihohin Sakkwato da Kano da Zamfara da Katsina da Jigawa da Kaduna da Kebbi), za su shiga gaba su ga an ceto wannan fanni. A ra`ayina, lallai lokaci ya yi da mahukuntan jihohi da na kananan hukumomi za su fara yekuwar jama`a su shiga fannin samar da ilmin `ya`yansu gadan-gadan, ta hanyar sa hannu  a cikin tafiyar da su tun daga tushe.
Zance ne kawai, a irin wannan lokaci mahukuntanmu su dage akan wai ilmi kyauta ne ga al`ummar da har gobe tana neman komai a yi mata kyauta koda kuwa za ta iya. Abin yi na farko shi ne, jama`a da kungiyoyin tsofaffin daliban makarantu, tun daga Firamare zuwa Sakandare su fara karbar makarantu daga mahukunta suna tafiyarwa da kansu da sunan al`umma, da wannan tsari na makarantun al`umma abokan zamanmu na kudancin kasar nan suka yi mana zara a wannan fanni, ta yadda a can kusan kashi 75 cikin 100, na makarantu suna hannun al`umma ne (al`ummar da kowa na ciki ba tare da bambancin addini ko kabila ko yare ba). Sabanin mu nan Arewa akasin haka ake da shi, wato kashi 75 zuwa 80,  cikin 100, na makarantunmu na mahukunta ne, saura na al`umma, wadda ko ita al`ummar za ka tarsa na kudi ne.
Ta samuwar haka ni ke jin za a iya kawo karshen ko rage matsalolin da yanzu makarantunmu suke fuskanta na rashin wadatattu kuma ingantattun gine-gine da kayayyakin koya da koyarwa da dakunan karatu da na gwaje-gwaje da sinadaran gwaje-gwajen da uwa uba kwararru kuma wadatattun Malamai da kuma kyautata jin dadin Malaman.
Idan da mahukuntan jihohi za su shige gaba su ga cewa koda a zaman gwaje sun kebe wasu makarantun Firamare da na Sakandare, sun shirya jama`a a yankuanansu, sun mika masu tafiyar da makarantun kacokan (amma dawainiya da Malamai dauka karin girma ladabtarwa biyansu albashi da alawus-alawus lalle su ci gba da kasancewa a karkashin kulawar Mahukunta). To, kuwa da a cikin wani dan karamin lokaci za a fara ganin canji.
Ko kusa ba cewa nike yi ba a soke makarantun kudi ba, a`a, abin da nike nufi shi ne iyaye da tsofaffin dalibai da masu hannu da shuni da uwa uba Sarakuna, lallai su yi ruwa, su yi tsaki cikin tafiyar da makarantun yankunansu. Idan da a ce  iyaye za su iya kashe koda rabin kudin da suke kashewa wajen biya wa `ya`yansu makarantun kudi cikin tafiyar da makarantun yankunansu, sannan kuma su zuba idanu wajen tafiyar da su, to kuwa da bunkasar ilmin da za mu gani a Arewa da ta ba kowa mamaki. Ai da haka `yan kudancin suka yi mana zara, wato yin komai a kungiyance. Yanzu shi ne lokaci, Allah Ya sa kuma mahukunta su shige gaba wajen ganin tabbatuwar hakan, don komai ake so al`umma su yi, to, kuwa sai da  jagorancin hukuma. A yanzu batun tabarbarewar ilmi laifinmu ne gaba daya, amma mahukunta suke kan gaba.