‘Faduwar Naira ba za ta sa a daga farashin siminti ba’
Gwamnatin tarayya ta ce faduwar darajar Naira ba za ta sa a daga farashin siminti ba. Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iwela ce ta bayyana haka a lokacin da take gabatar da jawabi yayin taron yadda za a mallaki fili da gidaje a ranar Talata a Abuja.Ministar ta ce a yanzu gwamnati tana ci gaba da […]
Gwamnatin tarayya ta ce faduwar darajar Naira ba za ta sa a daga farashin siminti ba.
Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iwela ce ta bayyana haka a lokacin da take gabatar da jawabi yayin taron yadda za a mallaki fili da gidaje a ranar Talata a Abuja.
Ministar ta ce a yanzu gwamnati tana ci gaba da tsare-tsaren hanyoyin da za su samar da kayayyakin gini a cikin gida masu rahusa.
Ta ce sai da gwamnati ta tattauna da Kamfanin dangote kafin ya rage farashin siminti.
“dangote ba zai kara farashin siminti ba duk da halin da muka samu kansu a ciki. Za a ci gaba da sayar da siminti a kan farashinsa na yanzu.”
Ta ce dangote ya yi alkawarin ba zai kara farashin siminti ba, saboda hakan zai rage hauhawar farashin kayayyakin gini.
Ta ce masana’antar gini tana daya daga cikin manyan masana’antun da suke bunkasa tattalin arzikin kasar nan, don haka za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta ci gaba da tsayawa da kafafunta.