Fafaroma zai amince da kafa kasar Falasdinu

A jiya Alhamis ne Fadar Fafaroma da ke birnin batican ta ce za ta amince da yarjejeniyar kafa kasar Falasdinu, kodayake, kasar Isra’ila ta ce ba ta ji dadin hakan ba, inda ta ce matakin zai kawo kafar angulu da kwanciyar hankalin da aka samu a yankin.  Tattaunawa tsakanin Falasdinawa da fadar batican abu da […]

Fafaroma zai amince da kafa kasar Falasdinu
Fafaroma zai amince da kafa kasar Falasdinu

A jiya Alhamis ne Fadar Fafaroma da ke birnin batican ta ce za ta amince da yarjejeniyar kafa kasar Falasdinu, kodayake, kasar Isra’ila ta ce ba ta ji dadin hakan ba, inda ta ce matakin zai kawo kafar angulu da kwanciyar hankalin da aka samu a yankin. 

Tattaunawa tsakanin Falasdinawa da fadar batican abu da aka kwashe fiye da shekara 20 ana yi, inda fadar take goyon bayan bai wa Falasdinawan ’yancin kafa kasar kansu a matsayin wata hanyar warware rikicin yankin.
Kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito, fadar ta damu sosai kan rikicin yankin ne saboda yadda kasar Isra’ila take ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa ciki har wurare masu tsarki na addinin Kirista.
Kodayake, wasu na kallon matakin da wani yunkuri da fadar ke yi domin kara yada addinin Kirista a yankin Gabas-ta-Tsakiya, a daidai lokacin da dubban Kiristoci Larabawa suke yin kaura daga yankin saboda guje wa tashe-tashen hankula.
Har ila yau, matakin na zuwa ne a lokacin da fafutukar kafa kasar Falasdinu take ci gaba da samun karbuwa, inda a bara Majalisar nahiyar Turai da ta Birtaniya da kasar Ireland da Spain da Sweden da kuma Faransa duka suka bayyana amincewarsu da ’yancin Falasdinawan.