Fahimtar alkiblar Buhari a cikin kwanaki 100
A cikin takardun da ke dauke da rahotannin kwamitin karbar mulki karkashin Ahmed Joda ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari cewa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da jihohi 27 ba su biya albashin ma’aikatan su ba har tsawon shekara guda. Kwamitin Joda ya shawarci shugaban kasa da cewa wannan lamari ne da ya kamata a […]
A cikin takardun da ke dauke da rahotannin kwamitin karbar mulki karkashin Ahmed Joda ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari cewa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da jihohi 27 ba su biya albashin ma’aikatan su ba har tsawon shekara guda.
Kwamitin Joda ya shawarci shugaban kasa da cewa wannan lamari ne da ya kamata a yi gaggawar daukar mataki.
Dalilin haka ne Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar biyan albashin, inda cikin watanni ukun da ya yi a kan mulki ya soma biyan wasu.
A ranar Asabar mai zuwa, 5 ga wannan wata, zai zama kwanaki dari da hawan Buhari mulki a karkashin jam’iyyar APC daidai da 29 ga Mayu, 2015, bayan da jam’iyyarsa ta zama jam’iyyar adawar farko da ta kada jam’iyya mai ci, a zaben da kowa ke ganin sa a matsayin sahihi.
Akwai mutane da dama da suka ce bai kamata a yanke hukunci kan rawar gani ko akasinta da gwamnatin ta taka cikin kwanaki 100 ba, kuma na amince da su. Amma tarihi ba zai manta ba. Don haka ba zan ce ban fahimci kwanaki 100 na mutumin da ke shugabancin kasa ba.
Buhari ya hau mulki bisa goyon bayan da ya samu daga maza da mata, musamman talakawa. Sabuwar gwamnatin ba ta samu goyon baya a wurin wasu masu hannu da shuni a kasar nan ba a yayin zabe, amma hakan bai hana shugaban kasar samar da tsaro ba, wanda ke da muhimmanci a harkar kasuwanci. Sabuwar gwamnatin ta gaji matsaloli da dama daga gwamnatin PDP, sakamakon rashin ingantacciyar gwamnati, wadda ta haifar da cin hanci da rashawa da rashin bin doka. Wadannan matsaloli sun kara kamari ne a karshen ‘yan shekaru biyu na Gwamnatin Goodluck Jonathan. A yayin da shugaban kasar yake ta kokarin bankado inda matsalolin suke, sashen mai na daya daga cikin manyan bangarorin da suka gurbace.
Na yi imani akwai hujjoji da dama a wadannan kwanaki 100, wadanda za su sanya a fahimci Gwamnatin Buhari da inda ta dosa. Ga kadan daga ciki. Zan ba da hakuri. Akwai wasu alkawurra da ake yadawa cewa Buharin ko APC ne suka rika yadawa a lokacin kamfen za a yi cikin kwanaki 100, amma ba a cika ba. Daftarin dai sunansa ‘’One Hundred Things Buhari Will Do in 100 Day.’’ Ma’ana, abubuwa 100 da Buhari zai yi a cikin kwanaki 100. Akwai ma wani daftarin kudirorin mai suna ‘’My Cobenant with Nigerians’’, wato alwashin da na sha wa ‘yan Najeriya.
A matsayina na daraktan yada kamfen din Muhammadu Buhari a lokacin, ban dauki nauyin a buga ko guda daya ba. Kuma ko rantsewa na yi, kaffara ba za ta hau kaina ba cewa, Buhari bai taba ganinsu ba. Sakamakon bayanan da wasu suka rika yadawa, cewa, da zarar Buhari ya hau mulki, ko hannu ya daga sama ko wata harara, to duk matsalolin da suka addabe mu za su gushe kafin kiftawar ido.
Amma duk da haka, Shugaba Buhari ya yi namijin kokari cikin wadannan kwanaki, har jama’a na cewa lallai an fara ganin canji, kuma mai sassaucin da ba a gani a baya ba.
Kun ga dai ya dawo da martabar tsarin aiki, tare da gudanar da ayyuka cikin nagarta, babu lalaci da sake. Ya sha fada ba sau daya ba, cewa akwai bukatar saisaita tsarin aikin gwamnati, don ba za a yarda da sakaci ba.
A jerin ayyukansa, har da kulla dangantaka da makwabta don shawo kan matsalar tsaro da kuma yadda za a ciyar da yankin Afrika gaba. Hawan mulkinsa da kwanaki hudu ya nuna kyawawan manufofin gwamnatinsa.
A ganawar sa da shugaban kasar Amurka, Barrack Obama, ya bayyana wa shugaban Najeriyar cewa yana kan turba mai kyau, kuma dole sai Najeriya na kan turba tagari kafin Afrika ta bi sawu.
Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, da ya kawo ziyara Najeriya, ya ce shugaban kasarmu na da kudirori masu kyau.
kulla dangantaka da kungiyar kasashe mafi karfin tattalin arziki na duniya, A tsarin tattalin arziki, Najeriya ta soma ganin ci gaban da ba za iya samu cikin kankanin lokaci ba.
Bai sa ko sisin kobo ba a bangaren wutar lantarki. Amma daga kamun ludayin mulkinsa ya nuna cewa ba za ka yi abin da ka ga dama a gwamnatin Buhari, har wutar ta zauna kaf a fadin kasar nan.
Wutar lantarki ta samu a wasu yankunan da ake samu fiye da tsarin da muke da shi na samar da wutar, domin shi ne babban kalubalen da kasar za ta fuskanta.
Tsarin tafiyar da kudin Najeriya ya sauya. Domin yanzu an samu asusun bai daya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa ido kan kudin gwamnati.
Bunkasa noma. Batun shigo da shinkafa ya ragu, kuma gwamnoni bakwai wadanda jihohinsu ke noman shinkafar sun tattauna da shugaban kan yadda za a bunkasa lamarin. Amurkawa sun yi alkawarin shigowa cikin harkar noman kasar a badi.
Ta’addancin Boko haram, da aka bari ya yi kamari cikin shekaru biyar, ya kusa kawo karshe, amma abin da ya fi ba da sha’awa shi ne, sanin makamar aikin da sababbin hafsoshin soja ya ba mu tabbacin cewa ‘yan matan Chibok za su dawo kamar yadda aka kwashe su.
Shugaba Muhammdu Buhari ya sha yabo a gida da waje kan yaki da cin hanci da rashawa. Ya fada tun a farko, cewa, gwamnatinsa ba za ta amince da wannan zaluncin ba.
Ya yi amfani da kalaman Firayiminstan Indiya, Narendra Modi: “Ba zan yi sata ba, kuma ba zan bari wasu su yi ba.” Haka kuma aka yi, domin Buhari yana kan cika alkawarin da ya dauka tun daga lokacin da ya hau mulki.
Shi da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, ba wai kawai rabin albashinsu suka zaftare ba, har ma da rage makudan kudin da ake kashewa a gidajensu da ofishoshinsu.
Haka kuma ya dauki muhalli da muhimmanci. Ya yi korafi cewa rashin tsaro a yankin Chadi ya kusan kafar da tafkin. Shugaban ya sha alwashin gyara Ogoniland, ta hanyar kwashe dagwalon mai, wanda ya gurbata musu muhalli.
A kasar nan, ana ta nadi da sauke wasu daga mukamai don ganin an kawo gyara a harkar gwamnati.
Sabuwar gwamnati ta kan sauke mutane daga mukamai ne don ba ita ta nada su ba, amma wannnan gwamnati ba haka take ba.
Gwamnatin Shugaba Buhari ba za ta bari ‘yan kama karya su tafiyar da kasar nan ba. Za a yi amfani ne da wadanda suka cancanta a wannan gwamnati.
Bai nada ministoci ba har yanzu, amma gwamnatin tana gudanar da harkokinta yadda ya kamata.
A wadannan watannin uku, gwamnatin tana bukatar jinjina kan samar da wutar lantarki, alaka da kasashen waje, yaki da ta’addanci da cin hanci da rashawa, inda Najeriya ta fara samun zaman lafiya, ba a tsakanin al’ummarta kadai ba, har da kasashen da take makwabataka da su da ma sauran kasashen duniya baki daya.
A wannan makalar, Shugaba Muhammadu Buhari zai zama kamar shugabanni irin su Lee Kuan-Yu da Firayiministan Indiya na yanzu, Narendra Modi’ da irin salon mulkinsa. Yana iya bambanta da su wajen gudanar da wasu harkokinsa na ci gaban kasa.
Malam Garba Shehu, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan yada labarai da hulda da jama’a.