Fahimtar da mata suka yi wa maza

Babu shakka rayuwar namiji ba za ta yiwu ba sai da mace, hakazalika rayuwar mace ba ta kammala, sai tare da namiji, saboda haka ne ake ganin cewa dukkansu sashe ne da ke taimakon sashe. Amma duk da haka wasu matan fahimtar da suka yi wa da namiji ta bambanta da yadda wasu suke kallonsa, […]

Fahimtar da mata suka yi wa maza
Fahimtar da mata suka yi wa maza

Babu shakka rayuwar namiji ba za ta yiwu ba sai da mace, hakazalika rayuwar mace ba ta kammala, sai tare da namiji, saboda haka ne ake ganin cewa dukkansu sashe ne da ke taimakon sashe. Amma duk da haka wasu matan fahimtar da suka yi wa da namiji ta bambanta da yadda wasu suke kallonsa, amma duk da haka ra’ayin matan ya bambanta, ya danganta da irin matsalar da ta shiga tsakaninta da namijin da take tare da shi.
Sau da yawa mata kan yi wa maza kudin goro wajen yanke hukunci ba tare da la’akari da bambancin da ke tsakani ba. Wasu matan kuwa son kai ne ke sa su yanke wa mazan hukuncin bai-daya. Misalan suna da yawa, amma na yi kokarin kawo kadan daga ciki.
Da farko mata sun dauki namiji a matsayin ba-dan-goyo-ba: Babu shakka Mafi yawan mata suna ganin namiji a matsayin wanda duk irin yadda suka amince da shi sai ya bata musu rai. Shi ya sa suke da karin magana da ke cewa namiji ba-dan-goyo ba ne. Amma wasu matan ba haka suka dauke shi ba, suna mutunta shi tare da yarda da shi.
Mace ta dauki namiji ma ci amana: Babu shakka wannan wata fahimta ce sananniya. Mata da yawa suna ganin duk irin amincewar da suka yi wa da namiji sai ya ci amanarsu. Ko dai ta hanyar yi musu kishiya ko kuma ma ya rabu da su baki daya, ko kuma ya karya musu zuciya yayin soyayya. Wasu kuwa sukan ba shi amana ba tare da gindaya masa ka’ida ba.
Sun dauki namiji Wawa: Da dama daga cikin mata sun dauki namiji a matsayin wawa wanda fahimtarsa tamkar ta yaro ce karami. Za ka ji suna cewa ai shi namiji sai yadda ka yi da shi, sai kuma yadda ka saba masa ba shi da wayon kansa. Ka ga ke nan shi namiji ba shi da tunanin na kansa, sai abin da mace ta nuna masa, kuma sai yadda ta yi da shi ke nan.
Wanda ba shi da sirri: Ita mace kullum gani take duk yadda ta bari namiji ya san sirrinta, to babu shakka sai ya tona mata shi, ya yada ta a duniya. Shi ya sa za ka ga wasu matan suna yi kafffa-kaffa da barin namiji ya san sirrinsu. Amma kuma sun manta cewa namiji shi ya fi mace rike sirri ba tare da bari wani ya tono shi ba.
Wanda bai san ya kamata ba: Da yawa za ka ji suna cewa su maza ai duk abin da ya zo musu a tunaninsu shi suke aikatawa ba tare da lura da a bin da zai zo ya komo ba. Amma wasu matan kuwa ba haka suka dauki namiji ba. Sun dauke shi mai tsananin sanin ya kamata da hangen nesa.
Marar lissafi: Wasu matan sun dauki namiji wanda ba shi da lissafi, musamman ma idan ya ga wata macen da yake so. Suna daukarsa a matsayin wanda idan yana son abu zai rika yi masa dawainiya babu lissafin irin riba ko akasin haka, ko alfanu ko rashin alfanun da zai samu ba. Amma wasu matan suna jinjina wa maza kan yadda suke da lissafi da kididdiga a kan al’amuran yau da kullum. Mata ba duka suka taru suka zama daya ba. Wasu matan sun san ya kamata wasu kuwa sai dai Allah Ya kyauta. Su ma mazan wasu sun san ya kamata wasu kuwa kare ba ya ci ba.
Za a iya tuntubar Haruna ta 08027406827, ko [email protected]