Fahimtar matakin CBN da Hukumar NDIC
Yawaitar samun rikice-rikice a bankuna a sassan duniya a shekaru masu yawa ya sanya gwamnati ta bullo da hanyoyin magance matsalolin. Yadda gwamnati ke shiga tsakani dangane da bankunan da suka ruguje ya zama ruwan dare a shekarun da suka gabata. Amfanin shiga tsakani na Bankin CBN da Hukumar Kare Ajiya a Bankuna (NDIC) kan […]
Yawaitar samun rikice-rikice a bankuna a sassan duniya a shekaru masu yawa ya sanya gwamnati ta bullo da hanyoyin magance matsalolin. Yadda gwamnati ke shiga tsakani dangane da bankunan da suka ruguje ya zama ruwan dare a shekarun da suka gabata.
Amfanin shiga tsakani na Bankin CBN da Hukumar Kare Ajiya a Bankuna (NDIC) kan bankin Skye za ta iya kasuwa gida biyu. Na farko don a tabbatar da kafuwar bankuna tare da kawar da rudani. Na biyu dawo da martabar bankuna tare da kare su daga fadawa mawuyacin hali.
Da yake karin bayani Manajan Hukumar NDIC ya ce “Ba kamar yadda idan banki ya ruguje ba da masu ajiya za su kasa samun kudin da suka ajiye, Bankin Bridge wato bankin da yake mallake bankin da ya ruguje yana bai wa masu ajiya tabbacin ci gaba da gudanar da asusun ajiyarsu tare da kaiwa ga kudinsu. Haka masu ajiya a bankin da ya durkushe bankin Bridge ne zai mallake kadarorinsa.
Baki daya dai bankin Bridge na tabbatar da ci gaba da ayyukan da bankin da ya durkushe ne yake yi a dukan rassansa tare da bai wa dukan masu ajiya tabbacin samun kaiwa ga ajiyarsu. Zai tabbatar da cewa ba ma’aikacin da ya rasa aikinsa saboda abin da ya faru. Mallake Skye Bank da Bankin Polaris ya yi zai ceci ayyuka dubu shida tare da tabbatar da gudanar rassan bankin Skye 300.
“Masu ruwa-da-tsaki sun yi asarar hannun jarinsu saboda jarin bankin ya ruguje kuma saboda kasa bunkasa jarin bankin Skye yayin da mahukunta suka nemi haka. Mambobin Hukumar Zartarwar Bankin wadanda suka janyo rugujewar bankin Skye za a bincike su tare da gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi
Ya kare da cewa ba za yi wasa da tabbatar da kafuwar tsarin bakuna ba. Kafa Bankin Polaris don ya maye gurbin Bankin Skye an yi shi ne don kare bukatun masu ajiya. An kafa Bankin Polaris ne don kare wadanda ke aiki a Bankin Skye da ya durkushe ta hanyar kare ayyukansu.