Fa’idar noman barkono da attaruhu ga mai karamin karfi
Kwalliya na biyan kudin sabulu domin shekara 20 yana noman attaruhu.
Mafi yawan noman barkono da attaruhu da ake yi a Najeriya, a Arewacin kasar ake yi, musamman a jihohin Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Sokoto da Filato da kuma Bauchi.
Kuma ba kamar wasu kayan lambun da aka saba nomawa a wadannan wurare ba, noman su yana da matukar amfani da fa’ida ga monomi ta musamman mai karamin karfi, ta fuskar kudin shiga da kuma karancin rikita-rikita da ka iya kai wa ga hasara, a cewar wasu manoman da suka gwada suka gani da kuma wadanda suka dade suna yi.
A cewar musu ruwa da tsaki a wannan sana’ar, noman Attaruhu na daya daga cikin hanyoyin da ke kawo riba mai yawa ga mai yin ta a cikin Najeriya da kuma wasu kasashe na duniya wadanda suka gano hakan.
Hakika noman attaruhu da kuma barkono na da riba kamar yadda noman tumatir da gurji yake.
Manoman barkonon sun ce, ribar noman nasu na da nasaba ne da yadda yaji yake da tasiri a tsakanin al’umma daban-daban da kuma al’adu mabambanta da hakan ya tilasta amfani da shi ta fuskar abinci da kuma wasu harkoki da suka shafi addini.
Bugu da kari, barkono da attaruhu na jure wahalar yanayi, za kuma a iya ajiye su tsawon lokaci ba tare da sun lalace ba.
Kuma saboda bukatarsu da ake yi a kasuwa, da wuya a yi musu ajiyar da za ta kai ga lalacewa kafin a sayar.
Ma’ana, a kowanne lokaci da akwai bukatar yajin barkono ko na attaruhu, wato bukatarsu ta fi samuwar su yawa, kusan komai a hannu-hannu yake.
A cewar Dauda Sunday, wani manomin attaruhu a Dorawar Babuje da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi ta Jihar Filato, manoman attaruhu ba su da hasara ko ta kwabo, saboda dalilai masu yawa idan aka kwatanta su da sauran masu noman kayan lambu irin su tumatir da gurji da kabeji da abarba da sauransu.
Ya ce, “Mai noman barkono ba ya bukatar jari mai yawa, kuma aikin noman ba shi da wahala sosai idan aka kwatanta ta shi da sauran kayan lambu da ke bukatar kudi da kuma kulawa, haka kuma ba ya bukatar taki da kuma maganin kwari da yawa,wanda suke da jan kudi mai yawa daga hannun manomi.
“Mu dai a wannan garin da wuya ka ga mun yi amfani da maganin kwari a shukarmu ta barkono ko attaruhu saboda kyawun kasar wurin da yadda ta ke habaka girman shuka.”
Mista Sunday ya kuma ce, manomin Attaruhu idan ya shuka yakan ciri ‘ya’yanta har sau 10 kafin shukar ta mutu baki daya.
Hakan na nufin za ka iya mai da kudinka ninkin ba ninki.
Idan ba ka samu wani abu ba a dibar fari, za ka iya samu a na biyu ko na uku.
Bugu da kari, da wahala ka kai barkononka ko attaruhunka kasuwa ka kuma dawo da shi gida saboda kasuwar ta yi nauyi ko baka sayar ba ko kuma farashi ya fadi, sai ka ajiye abinka, har sai lokacin da ka ga dama, domin ba zai lalace ba saboda ajiya.
Sai ma ka busar da shi idan kana so, wanda hakan zai sa a siye shi da tsada.
Sannan ya kuma kara da cewa, noman barkono ko attaruhu na mai karamin karfi ne.
“Hakika noman barkono na wanda ba shi da jarin da zai sa a noman da zai ja kudi da yawa ne. Ba ina nufin attajirai ba za su iya ba ne, ina nufin noman ba ya bukatar manyan kudi na a-zo-a-gani.
“Ni dai ina son noman barkono saboda saukin jarinsa da kuma ribarsa mai yawa cikin sauki. Ni dai na amfana da noman, domin sama da shekaar 10 ina yi, ban kuma taba faduwa ba”.
Shi ma wani manomin attaruhu a garin na Dorawar Babuje mai suna Chiristopher Chollom ya ce, kwalliya na biyan kudin sabulu domin shekara 20 yana noman attaruhu kuma yana ganin saukin da yake samu da kuma fa’ida, sai ya bayar da misali: “Idan ka shuka tumatir ba ka sa masa taki a lokcin da ya kamata ba, to zai lalace, za kuma ka yi hasara duk aikin da ka yi masa.
“Amma shi attaruhu za ka iya shuka shi ba tare da ka sa masa taki ba har na tsawon wata guda, babu abin da zai same shi.
“Da kuma zarar ka samu sukuni, ka sa masa taki sai ya kama, ya kuma ci gaba da girma.”