Fa’idojin aure:
Jama’a bayan gaisuwa da fatan alheri. A wannan makon kuma za mu tattauna ne a kan fa’idojin aure, da hikimomin da suke kunshe a cikinsa. Daga: Nata’ala Sambo Babi (Nasaba) Aure yana da fa’idoji da hikimomi masu dinbin yawa, wadanda daga cikinsu akwai kare kai daga fada wa halaka ta hanyar aikata alfasha. Ku sani […]
Jama’a bayan gaisuwa da fatan alheri. A wannan makon kuma za mu tattauna ne a kan fa’idojin aure, da hikimomin da suke kunshe a cikinsa.
Daga: Nata’ala Sambo Babi (Nasaba)
Aure yana da fa’idoji da hikimomi masu dinbin yawa, wadanda daga cikinsu akwai kare kai daga fada wa halaka ta hanyar aikata alfasha. Ku sani ya ku ’ya ’ya mata cewa, kowane dan’adam akwai wata halitta ta sha’awa, wadda Allah ya sanya a tsakanin mace da namiji idan suka balaga. Wadda kuma idan ta motsa wa dayansu, mace ko namiji to, hakika sai dayansu ya ga ya kawar da wannan sha’awar sannan zai sami kwanciyar hankali. kuma idan dayansu ya ce zai kau da wannan sha’awar, to matukar ba shi da aure, to sai dai idan zai aikata haramun, ma’ana sai dai idan zai yi zina. kuma Allah ya hane mu da mu aikata a cikin littafinSa Ya yi mana gargadi cewa, kada mu kusance ta balantana mu kai ga aikata ta,Allah subhanahu wa ta’ala Ya ce:”Kuma kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfãsha ce kuma ta mũnana ga zama hanya”. Suratul Isra’i aya ta 32. Kun ga ke nan ta hanyar aure ne kawai, mace da namiji za su sami kau da wannan sha’awa ta hanyar halal, wadda kuma ba haramci ko karahanci a cikinta, kai hasalima za a ba su lada, wato ga lada ga la’ada ke nan.
Haka ma daga cikin fa’idojin yin aure akwai tabattar da alaka ingantacciya tsakanin mace da namiji, haka ma da kara dankon zumunci tsakanin dangin mata da miji. Sannan kuma, akwai wani bayani da majalisar dinkin duniya ta fitar tun shekaru 55 da suka wuce, wanda jaridar Sahafattush Sha’aban ta fitar cewa, an tabbatar da cewa, hakika alakar ma’aurata da rayuwarsu ta fi ko wacce alaka dadewa da tabbata. Wadannan ma’auratan samari ne da ’yan mata ko kuwa zawarawa ne, kai ko ma tsofaffi ne, dukkansu idan suka kulla alaka ta aure wannan alaka ta rayuwa ta fi ko wacce alaka inganci da dadewa.
To ya ku ’yan uwana mata da maza, mu duba a nan fa wadanda ba musulmi ba ne suka fadi wannan maganar. To balantana kuma mu musulmi mai za mu ce a kan hakan. Kasancewar ma mu ne muke tare da littafin da yake bayanin dukkan wani tsari wanda ya dace da dan’adam, mai amfani da marar amfani. Wanda kuma wannan littafin ya yi cikakken bayani a kan aure da muhimmancinsa da alkhairan duniya da na lahira.
Haka kuma daga hikimar aure akwai samun zuriya, wadda za ta yawaita. kuma da samun ladan bin umarnin Ma’aiki sallallahu alaihi wa sallam da yake cewa: “ Ku yi aure ku hayyayafa domin na yi alfahari da ku a ranar alkiyama’’. Mutum zai sami soyayyar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam saboda ya taimaka al’ummar Manzo ta yawaita a doron kasa wadda Annabi ya ce zai yi alfahari da ita a ranar alkiyama.Haka ma mutum zai sami albarkar addu’ar da dansa zai yi masa bayan mutuwarsa.
Sai dai a wannan zamanin da al’ammura suka lalace, ’yan matanmu sun ari bakin al’adu na Turawa wadanda suke hanun riga da na addinin Musulunci. Ta bangare daya kuma, ya ke ’ya mace idan kika lura ai dole ne ma ki yi kokari na ganin mahaifanki sun aurar da ke, kasancewar yanayin da muka tsinci kawunanmu a ciki. Turawa sun bijiro mana da abubuwan da ke sanya motsa sha’awa ga su nan da dimbin yawa. Ga abubuwan kallo ba adadi, yau fina-finan batsa sun yi yawa kamar jamfa a Jos. Kuma na san a yau ’yan matanmu na wannan zamanin mafi yawa daga cikinsu duk suna dauke da wadannan nau’uka na fina-finai. Ko kuma idan ke ba ki da su,to akwai su a cikin wayar kawarki. Kuma yau da gobe sai ki nemi ta saka miki su. Domin zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai.
Kuma yau fita zuwa wajen kawaye, da fita kasuwa ya zamar wa ’yan matanmu wajibi saboda haka dole ne ki ga saurayin da ya burge ki, daga nan kuma sai ki tuna da wani fim da kika taba kalla, sai kuma ki fara sha’awar namiji.Kin ga idan kina da mijinki halalinki, kai tsaye sai ki wuce zuwa gida ya kawar miki da wannnan sha’awar da ta motsa miki. Kuma Allah ya ba ki lada.
Haka kuma kowa ya san irin tashe-tsahen hankulan da ake ciki a wannan kasar. Abin nufi a nan shi ne kowane lokaci rigima takan iya tashi a inda kike har ta yi sanadiyar rasa rayuwarki. Kin ga ya kamata ki yi kokarin ganin kin yi aure kafin naki wa’adin ya yi. Ko da ba ki haihu kin bar zuriya ba, ai kin dai yi ibada saboda kin cika umurnin Allah, da na ManzonSa. Sai ki hadu da Allah kina fatan samun rahamarsa. Idan kuwa kin haihu ,to idan babu ke sai a rika ganin abin da kika bari a tuna da ke a yi miki addu’a. Kuma idan ya girma ya rika yi miki addu’a. Kuma mijinki da ’yan uwan mijinki, idan har kin yi mu’amalar kirki da su sai su rika yi miki addu’a. kari da wadda iyayenki za su rika yi miki.
Ya ke ’yar uwa ki ji tsoron Allah ki yi aure, kada ki ce wai ke sai kin kammala karatu za ki yi aure, ko kuma sai kin girma za ki yi aure, ko sai kin tara abin duniya za ki yi aure. To idan kuma kika mutu a kokarin tara abin duniyar fa, ko kuma har lokaci ya kure miki kuma ba ki sami abin da kike so ba. kuma ba ki yi auren ba, kin yi biyu babu ke nan.Saboda haka ya kamata ki sani cewa aure ba ya hana karatu matukar kun fahimci juna ke da mijinki, Allah dai ya shirye mu.
Za a iya samun Nata’ala a 080 63 67 36 56